Rundunar ‘yan sandan Nijeriya a ranar Juma’a ta tabbatar da kama wasu jami’anta biyu masu mukamin kwanstabul kan zargin karbar rashawa daga wata Baturiya. Lamarin ya faru ne a kan hanyar Iseyin zuwa Ogbomosho da ke Jihar Oyo.
A wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, an ga wasu ‘yan sanda biyu sun tsayar da wata Baturiya wadda ta ce ta taho tun daga kasar Netherlands a kan babur wadda ta ce za ta je Abuja.
A cikin bidiyon, an ji ‘yan sandan suna tambayar Baturiyar me ta kawo musu bayan haka kuma aka ji suna rokonta kudi cikin raha. Sai dai a sanarwar da mai magana da yawun ‘yan sandan Nijeriya Muyiwa Adejobi ya fitar a ranar Juma’a, ya bayyana cewa an kama ‘yan sandan ne saboda halayyar da suka nuna ta rashin kwarewar aiki.
Adejobi ya kuma tabbatar da cewa tuni kwamishinan ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Oyo Adebola Ayinde Hamzat ya tanadi tsarin ladabtarwa kan lamarin ba tare da bata lokaci ba.
“Hukumar ‘yan sanda ta yi Allah-wadai da wannan aika-aika tare da ba da umarnin hukunta ‘yan sandan da kuma shi kansa jami’in ‘yan sandan da ke sa ido a kan su.”
Sanarwar ta kara da cewa rundunar ‘yan sandan kasar za ta ci gaba da matsa kaimi wurin gudanar da shirye-shirye na sake wayar da kai da horo ga ‘yan sanda domin guje wa afkuwar irin wannan lamarin.
Zargin rashin ɗa’a ga ‘yan sanda
Ba wannan ne karon farko da rundunar ‘yan sandan Nijeriya ke fitar da sanarwar zargin jami’anta da rashin ɗa ba.
Ko a kwanakin baya sai da rundunar ‘yan sandan ta yi tir da halayen wasu jami’an nata bayan wani bidiyo ya nuna wasu jami’anta sun bi ta kan wani mutum da mota.
Haka ma a kwanakin baya rundunar ‘yan sandan ta sallami wasu jami’anta uku da ke ba mawakin nan na Nijeriya Dauda Kahutu Rarara kariya sakamakon laifukan da suka hada da amfani da bindiga ba bisa ka'ida ba da wuce gona da iri da rashin ɗa'a