Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta tabbatar da cewa ta kama wasu jami'anta da ke bai wa shahararren mawakin nan na Kano Dauda Kahutu Rarara kariya.
A wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, an ga ‘yan sandan suna bin mawakin a baya har ya shiga mota bayan haka suka soma harba bindiga a sama.
Sai dai a wani sako da kakakin 'yan sandan Nijeriya Muyiwa Adejobi ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Asabar, ya ce rundunar ‘yan sandan kasar ta yi tir da “rashin kwarewa da rashin ɗa’a da ‘yan sandan suka nuna inda suke harba bindiga domin kuranta mawakin na Kano.
“An gano ‘yan sandan kuma an kama su. Za a kai su hedikwatar ‘yan sanda domin yi musu tambayoyi da daukar matakan da suka dace,” in ji shi.
Ya kara da cewa irin wannan ɗabi’a ba ta ‘yan sanda ba ce kuma ba za su lamunci hakan ba.
Ɓata-gari
Sai dai wata hira da aka yi da mawakin, ya ce 'yan sandan sun yi harbi ne bayan da suka samu labarin cewa wasu bata-gari za su yi tarzoma yana mai cewa ba don nishadi suka yi harbi a iska ba.
“Mun je muna rabon abinci a Kahutu, sai wasu bata-gari suka shigo suna neman su tayar da tarzoma, a nan wurin ne muka samu matsala ‘yan sandanmu suka yi harbi sama,” a cewar Rarara.
Ya bayyana cewa ‘yan sandan ba su harba hayaki mai sa hawaye ba saboda ana azumi.
A kwanakin baya ne dai wasu matasa suka far wa gidan mawakin a Jihar Kano inda suka kona wani sashe na gidan tare da kwashe wasu kayayyaki.
Sai dai daga baya ‘yan sanda sun samu nasarar gano wasu matasan da kuma kwato kayayyakin.
Mawakin ya shahara wurin yin zagi a wakokinsa musamman ga 'yan siaysar da ba ya goyon bayansu.