'Yan sanda a Afirka ta Kudu sun ce sun kama 'yan Nijeriya su takwas bisa zargin ta da fitina da ɓarnata kadarori, bayan da suka far ma 'yan sanda.
Waɗanda ake zargin sun lalata motocin 'yan sanda kuma suka fasa tagogin ofishin 'yan sanda na Kimberley a daren Alhamis.
'Yan sandan sun ce waɗanda aka kama ɗin sun kawo harin ɗaukar fansa ne bayan da jami'ansu suka kama wani ɗan Nijeriya kan zargin mu'amala da miyagun ƙwayoyi.
Kakakin Gundumar SAPS, Cherelle Ehlers ta ce, "Lokacin aiwatar da kamen, wanda aka zo kamawa ya yi yunƙurin bijirewa, kuma ya doki jami'an SAPS ɗin da bulalar taya. Wasu gungun mutane da ake kyautata zaton 'yan Nijeriya ne sun far wa jami'an suka lalata motocinsu."
Jami'ar ta ƙara da cewa, "'Yan sanda sun harba harsashin roba don tarwatsa mutanen... a yayin hakan, mutanen sun fasa tagogin caji ofis ɗin. Gungun mutanen sun tunkaro ofishin kuma suka yi barazanar ɗaukar fansa.
"Kwamandan samamen ya gargaɗi mutanen da su watse. Sannan bayan tafiyarsu, mutanen sun lalata motocin 'yan sanda... kuma an kama ƙarin mutane huɗu bisa zargin ɓarnata kadarori."
Kwamishinan 'Yan Sanda na Gundumar Northern Cape, Laftanal Janar Otola ya yi Allah-wadai da wannan ɗabi'a, kuma ya jaddada cewa duk wanda ya hana 'yan sanda aiwatar da ayyukansu za a hukunta shi bisa doka.
Otola ya ƙara da cewa, "Ba za mu bar irin wannan ɗabi'a ta yi wa doka karan-tsaye ba; muna aiki tare da Ma'aikatar Cikin gida don tantance ko waɗanda ake zargin suna da halaccin zama a ƙasar nan.
"Ƴan sanda za su ci gaba da ɗabbaƙa ƙarfin hukumar ƙasa a Gundumar Northern Cape."