Gwamna Dhadho Godhana ya gabatar da kansa a hedikwatar hukumar binciken laifuka ta DCI ranar Asabar. / Hoto: AFP

Wani gwamnan lardi a Kenya ya shiga hannu sakamakon faɗa da ake yi tsakanin ƙabilu a yankin bakin ruwa na lardin Tana River, inda aka halaka mutane da dama.

An kama gwamna Dhadho Godhana, tare da wani ɗan majalisa na yankin, saboda ƙin amsa gayyatar da aka musu kan faɗan, a cewar 'yan sanda ranar Asabar. Mutanen biyu ba su ce komai ba kan zarge-zargen.

Aƙalla mutane 14 ne aka kashe a faɗace-faɗace a kudu maso gabashin Kenya, abin da ya janyo hukumomi suka ayyana yankunan biyu a lardin a matsayin masu haɗari, kuma marasa tsaro, har zuwa nan da kwanaki 30.

An tsaurara tsaro a yankunan kuma an haramta wa mazauna yankin fita da makami, cewar maƙalar doka da ma'aikatar cikin gida ta fitar.

An tuhumi gwamna

Gwamna Godhana ya gabatar da kansa da safiyar Asabar a hedikwatar hukumar binciken laifuka ta Directorate of Criminal Investigations (DCI), da ke babban birnin ƙasar, Nairobi. Kuma ana masa tambayoyi game da rikicin, cewar shugaban hukumar DCI, Mohamed Amin.

Shafin Citizens News ya ambato shi yana cewa, “Muna sa ran gabatar da waɗanda za a samu da laifi a gaban kotu, kan abin da ke faruwa a Tana River, bayan mun gama bincikenmu.”

Tuni an yi sammacin 'yan siyasa biyar daga lardin Tana River don su gabata gaban hukumar haɗa kan jama'a ta National Cohesion and Integration Commission (NCIC), ranar Litinin, don amsa tambayoyi kan zarge-zargen ruruta rikici tsakanin al'ummomi biyu.

Yankin Tana River ya fuskanci rikice-rikicen ƙabilanci mai alaƙa da taƙaddama kan wurin kiwon shanu, wanda ya haifar da mutuwar gomman mutane.

TRT Afrika