Rundunar ƴan sandan Jihar Kano da ke arewa maso yammacin Nijeriya ta ce ta kama mutum 29 ɗauke da makamai da kayan maye a lokacin bikin Maulidi na Takutaha da aka yi a fadin birnin ranar Alhamis.
A wani sakon bidiyo da mai magana da yawun rundunar Abdullahi Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce ana zargin waɗanda aka kama da yunƙurin tayar da zaune tsaye.
“Tun da farko gabanin hidimomin Maulidi Kwamishinan ƴan sanda na Jihar Kano CP Usaini Gumel ya ja hankalin al’umma da cewa su bi doka da oda a lokacin cewa duk wanda ya san zai fito don ta da hankalin al’umma to kuwa an baza jami’an tsaro don yin kame,” in ji ASP Kiyawa.
Rundunar ƴan sandan ta Jihar Kano na yawan yin holen mutanen da take kamawa bisa zarginsu da aikata miyagun laifuka kamar ƙwace wayoyi da dabanci da shaye-shaye da sauran su.
Kuma ana yawan samun tashe-tashen hankula a lokutan bukukuwan al’ada da na addini, inda masu son tayar da zaune tsaye ke amfani da damar don cutar da mutane.
Rundunar ƴan sandan ta ce ta kama mutum 29 ɗin ne a lokacin Takutahar a wurare daban-daban ne a fadin jihar, kuma suna ɗauke da muggan makamai da kayan maye.
A bidiyon da Kiyawa ke bayani an ga makaman da rundunar ta baje a gaban wadanda aka kama din a hedikwatar ƴan sanda da ke Bompai.
“Makaman da aka kama su da su sun haɗa da wuƙaƙe da almakashi da ɗan bida da adduna da wiwi,” in ji Kiyawa.
Rundunar ƴan sandan ta sa wasu daga cikin mutanen, wadanda dukkansu matasa ne ƴan tsakanin shekaru 18 zuwa 25, sun yi bayani kan yadda aka kama su da kuma irin makaman da suke riƙe da su.
“A yanzu haka mutanen suna babban sashen binciken manyan laifuka don yin bincike, sannan a gurfanar da su a gaban kotu,” a cewar mai magana da yawun ƴan sandan.