Maharan sun kai hari cikin barikin sojoji da kuma gidan yari. / Hoto: Reuters

Shugaban Saliyo Julius Maada Bio ya bayyana cewa jami’an tsaro sun kama “akasarin shugabannin” wadanda suka yi kokarin hargitsa kasar.

Ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi wa 'yan kasar ta gidan talbijin ranar Lahadi da maraice.

“An kama akasarin shugabanninsu. Ana ci gaba da gudanar da bincike,” kamar yadda shugaban kasar ya bayyana.

Wannan na zuwa ne bayan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai barikin sojoji inda suka fasa wurin da ake ajiye makamai. Haka kuma maharan sun fasa gidan yarin kasar inda suka saki fursunoni.

Hadin kan kasa

Shugaba Bio ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta tabbatar an hukunta wadanda aka kama da laifi bayan an bi ka’ida.

Ya kuma yi kira ga ‘yan kasa su hada kansu inda ya ce “karfinmu ya dogara ne kan hadin kanmu” inda kuma ya tabbatar wa ‘yan kasar cewa gwamnatinsa za ta samar da zaman lafiya da tsaro a cikin kasar.

Kungiyar ECOWAS ta nuna rashin jin dadinta kan lamarin da ya faru a Saliyo a ranar Lahadi.

“Kungiyar ECOWAS ta ji labarin wannan abin kyamar da wasu mutane suka dauki makamai da niyyar kawo cikas ga zaman lafiya da kuma dokar da kundin tsarin mulki ya tanada a Saliyo,” kamar yadda kungiyar ta bayyana a wata sanarwa.

“ECOWAS ta yi Allah wadai da wannan lamarin inda take kira kan a kama tare da hukunta wadanda suke da hannu a lamari. ECOWAS na kara jaddada cewa ba za ta lamunci sauyin gwamnati ba bisa ka’idar kundin tsarin mulki ba.”

TRT Afrika