Rundunar 'yan sandan Ghana ta ce ta kama mutum hudu da ake zargi sun ci zarafin wani jami'inta.
A kwanakin baya ne wani bidiyo ya karade shafukan sada zumunta inda aka ga wasu matasa suna lakada wa dan sandan duka har suka ci karfinsa suka kwace bindiga da wayoyinsa.
A wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta Ghana ta fitar ranar Lahadi, ta ce bayan ta samu rahoton yadda lamarin ya faru a ranar 8 ga watan Maris na 2023, ta kaddamar da bincike da ya kai ta ga kama mutum hudu daga cikin wadanda ake zargi.
Rundunar ‘yan sandan ta ce mutanen da ta kama sun hada da Kojo Siah wanda aka fi sani da Mozey, da Emmanuel Mensah wanda aka sani da Kofi Asamoah, da Maxwell Cudjoe da kuma Agyabu Haruna Dissawu.
Rundunar ta kara da cewa ta gudanar da bincike a gidan daya daga cikin wadanda ake zargi wanda har yanzu ake nema ruwa a jallo mai suna Kwame Ato Asare Ani inda aka gano bindiga kirar ‘Pump Action’ guda uku.
Kazalika ta ce an sake gano wata bindigar ‘Pump Action’ guda daya da adduna biyu a cikin motarsa wadda ba a yi wa rajista ba.
Sauran abubuwan da aka gano sun hada da harsasai biyu da kuma babur daya wanda ba a yi wa rajista ba.
Rundunar ‘yan sandan ta ce tuni aka kai wadanda ake zargin a gaban kotu kuma za ta ci gaba da neman wadanda ake zargi da wannan lamari.
A makon jiya ma ‘yan sandan sun kama mutum uku dauke da makamai ba bisa ka’ida ba a Japa da ke Yammacin Ghana.