Jami'an hukumar ‘yan sanda mai yaki da masu safarar miyagun kwayoyi wato OCRTIS a Jamhuriyyar Nijar, ta yi nasarar kama wasu matasa uku a garin Gaya na Jihar Dosso dauke da daurin tabar wiwi 917 da nauyinta ya kai kilogiram 812.5.
Wannan kame na zuwa ne kasa da mako guda bayan hukumomi sun yi makamancin wannan kamen a kasar.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Laraba, ta ce an kiyasta kudin wiwi din inda ya kai CFA 36,680,000, kwatankwacin dala 62,000.
An shigar da wiwi din ne ta hanyar Kogin Isa cikin garin na Gaya na kan iyakar Jamhuriyyar Benin da Nijeriya, inda matasan suka yi niyyar jigilarta zuwa Nijeriya da wasu garuruwa na kasar Nijar.
Masu sharhi na cewa masu safarar miyagun kwayoyi na son mayar da Jamhuriyyar Nijar hanyar tsallakawa da hajojinsu zawu wasu kasashen yamma.
Mai magana da yawun hukumar ‘yan sanda ta kasar, Abou Mountari ya ja hankalin ‘yan kasar da su ci gaba da bai wa jami'an tsaron hadin kai don yakar masu wannan “muguwar sana'ar”.