Rundunar 'yan sandan ta ce tuni ta mika magungunan ga NAFDAC. Hoto/Abdullahi Haruwa Kiyawa

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta ce ta kama lalatattun magunguna da kuma magunguna na bogi.

‘Yan sandan sun samu gano wadannan magungunan ne bayan sun samu bayanan sirri.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sandan reshen Jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, an gano magungunan ne a wasu manyan dakunan ajiyar kayayyaki guda biyu da ke kasuwar Mallam Kato.

Magungunan da aka kama sun hada da kwalaye 514 na magungunan ruwa na Emistxmin/Emstifer da kwalaye 219 na magungunan kwaya na Lisinopril 5mg, sai kwaleye bakwai na Amlodipine 5mg.

Sai kuma kwalaye 87 na Atenol 50mg da kwalaye 120 na wasu hadin magunguna da kwalaye 40 na wasu.

Haka kuma rundunar ‘yan sandan ta kama kwalaye uku na allurar Frusemide.

Rundunar ‘yan sandan ta ce tuni ta mika duka wadannan kwalaye ga hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasar wato NAFDAC.

TRT Afrika