Rundunar ‘yan sandan kasar Ghana ta soma bincike kan mutuwar wani jami’inta mai mukamin kwanstabul wanda ake zargin wani abokin aikinsa da ke gabansa a mukami ya harbe shi a yankin Gabashin Yammacin Ghana.
A wata sanarwa da mataimakiyar daraktar watsa labarai ta ‘yan sandan Ghana Grace Ansah-Akrofi ta fitar, kwanstabul din ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da suke dawowa daga aiki a ranar Juma’a da dare, inda ake zargin abokin aikinsa ya harbe shi.
“An garzaya da shi asibiti domin a duba lafiyarsa, amma an sanar da cewa ya rasu ko da aka kai shi asibitin,” in ji sanarwar.
‘Yan sandan ba su bayyana dalili ko kuma yadda aka yi har abokin aikin nasa ya harbe shi ba, amma ta ce tuni aka kama wanda ake zargin inda ake gudanar da bincike a kansa.
Tuni babban sufeton ‘yan sandan kasar ya aika da tawagar ‘yan sanda daga Accra babban birnin kasar domin bincike kan lamarin, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Haka kuma babban sufeton ya sake aikawa da tawaga ta musamman domin ta’aziyya ga iyalan dan sandan da ya rasu.
Ko a watan da ya gabata sai da aka kama wani dan sanda a Ghana bisa zarginsa da kashe wata wadda ake zargin budurwarsa ce.