'Yan sanda a kasar Ghana sun kama karin mutum hudu bisa zarginsu da kai hari ga 'yan sanda a yankin Yammacin kasar.
Wannan kamun da aka yi ya sa jumullar wadanda ke hannu bisa zarginsu da aikata laifin ya kai mutum takwas.
Wadanda ake zargin sun kai hari ne ga 'yan sanda wadanda suke shawagi domin tabbatar da tsaro a gundumar Axim a Yammacin Ghana a ranar 9 ga watan Maris.
Karin mutum hudun da aka kama sun hada da Kwame Ato Asare wanda aka fi sani da Kwame Ani sai Williams Kwofie da Richard Kwesi sai kuma Kojo Bronie.
A kwanakin baya ne wani bidiyo ya karade shafukan sada zumunta inda aka ga wasu matasa suna lakada wa dan sandan duka har suka ci karfinsa suka kwace bindiga da wayoyinsa.
Bayan haka ne rundunar 'yan sandan ta kaddamar da samame inda ta kama mutum hudu a karon farko.
A wata sanarwa da rundunar 'yan sandan ta Ghana ta fitar, ta ce karin mutum hudun da aka kama sun shiga wasan buya da 'yan sanda ne tun bayan da suka kai hari kan jami'ansu, amma an kama su a wani kauye kusa da kauyen Enchi da ke yankin Yamma maso Arewaci a kasar.
'Yan sandan sun bayyana cewa daya cikin wadanda aka kama Kwame Ato Asare a lokacin da yake boye, ya yi hira da gidan jaridu da dama inda ya yi zargin cewa kwamandan 'yan sadan gundumar da sauran 'yan sandan suna karbar kudi daga wurin jama'a.
Rundunar 'yan sandan ta ce ta soma bincike kan wannan zargin kuma duk wani dan sanda da aka samu da laifi zai fuskanci fushin hukuma.