Sojoji da 'yan sanda na yi sintiri a Maputo babban birnin kasar Mozambique da sanyin safiyar Alhamis gabanin zanga-zangar adawa da sakamakon zaben da 'yan adawa suka ki amincewa da shi.
Rikici ya matuƙar girgirza ƙasar da ke kudancin Afirka tun bayan da Jam'iyyar Frelimo wadda ta shafe shekara 50 tana mulki ta lashe zaɓe a ranar 9 ga watan Oktoba.
Birnin mai sama da mutum miliyan guda ya kasance shiru a ranar Alhamis da safe sakamakon an rufe shaguna da makarantu da jami'o'i.
Gomman masu zanga-zanga sun taru a ɗaya daga cikin manyan titunan birnin kafin wani soja ya shaida musu cewa kowa ya koma gida
Sakamakon zaɓen da ake rikici a kai
Daniel Chapo na Jam'iyyar Frelimo ya yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa da kaso 71 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa, kamar yadda hukumar zaɓe ta tabbatar, inda babban abokin hamayyarsa Venancio Mondlane ya zo na biyu da kaso 20.
Mondlane wanda ke da goyon bayan Jam'iyyar Podemos wanda ya ce sakamakon na ƙarya ne kuma shi ne ya ci zaɓe ya yi kira da a gudanar da zanga-zanga a ranar Alhamis.
Ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta, ya jawo magoya bayansa sun fito a kan tituna lamarin da ya jawo rikici.
A wata hira da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, jagoran 'yan adawar, wanda ba a san inda yake ba, ya ce ba zai halarci zanga-zangar ba saboda damuwa da lafiyarsa.
An kashe aƙalla mutum 18
Akalla masu zanga-zanga 18 ne aka kashe a rikicin da ya biyo bayan zaben kasar, a cewar kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch.
Wata ƙungiya mai zaman kanta ta cikin gida, Centre for Democracy and Human Rights (CDD), ta ce adadin wadanda suka mutu ya kai 24.
An kuma kashe wani ɗan sanda a wata zanga-zangar da aka yi a karshen mako, kamar yadda Ministan Tsaro Cristovao Chume ya shaida wa manema labarai a ranar Talata, yana mai gargadin sojojin na iya shiga tsakani "domin kare muradun jihar."
"Akwai aniyar sauya gwamnatin da aka kafa ta hanyar dimokuradiyya," in ji shi, a daidai lokacin da ake fargabar cewa shugaba mai barin gado Filipe Nyusi na iya ayyana dokar ta baci.
Ana sa ran Nyusi zai sauka daga mulki a farkon shekara mai zuwa a karshen wa'adinsa na biyu.
Katse hanyoyin intanet
Hukumomin kasar sun katse hanyoyin intanet a duk fadin kasar a wani abu da ya zama tamkar wani yunkuri na "murkushe zanga-zangar lumana da sukar gwamnati," a cewar kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch (HRW).
"Rufewar ya hana mutane damar karba da amfani da samun bayanai na ceton rai, da haduwa cikin lumana, da bayyana ra'ayoyinsu na siyasa a lokacin da ake cikin rikici," in ji Allan Ngari, darekta a ƙungiyar HRW.
Babban jami'in kare hakkin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya Volker Türk, ya shaida a ranar Laraba cewa "ya damu matuka da rahotannin tashe-tashen hankula a fadin kasar."