Wannan lamarin na zuwa ne ƙasa da makonni biyu bayan gudanar da zaɓen ‘yan majalisa a ƙasar / Hoto:Reuters

An ji ƙarar harbe-harben bindiga da yammacin Laraba a kusa da fadar shugaban kasa a N'Djamena babban birnin kasar Chadi. Rahotanni sun ce an jibge tankokin yaki da jami'an tsaro a kan tituna.

Wata majiyar tsaro ta ce wasu mutane ɗauke da makamai sun kai hari a cikin harabar fadar shugaban kasar, sai dai mai magana da yawun fadar shugaban ƙasar Abderaman Koulamallah ya ce komai ya lafa.

An toshe dukkan hanyoyin da ke zuwa fadar shugaban kasa, ana kuma iya ganin tankokin yaki a kan titunan babban birnin kasar, kamar kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

Wannan lamarin na zuwa ne ƙasa da makonni biyu bayan gudanar da zaɓen ‘yan majalisa a ƙasar.

Tsamin dangantaka da Faransa

Kasar Chadi na cikin kasashen Afirka da a baya-bayan nan ta shiga cikin jerin ƙasashen Afirka da suka juya wa Faransa baya.

A ranar 6 ga watan Janairu, Chadi ta caccaka shugaban Faransa Emmanuel Macron kan kalaman da ya yi game da Afirka.

Shugaba Macron, wanda kasarsa ke fuskantar koma baya a nahiyar Afirka, ya ce shugabannin Afirka sun "manta ba su gode wa" Faransa ba saboda "taimakawa wajen yaki da ta'addanci a yankin Sahel."

Macron ya bayyana hakan ne ga jakadun Faransa a yayin taron shekara-shekara na kasar kan manufofin ketare a birnin Paris.

AFP