A watan Janairu ne aka kashe dan jarida Martinez Zogo a birnin Yaounde/Hoto:Reuters

Rahotanni daga birnin Bamenda da ke arewa maso yammacin Kamaru na cewa an harbe wani dan jarida.

An harbe Anye Nde Nsoh da ke aiki da jaridar the Advocate ne a wani shagon sayar da barasa a unguwar Ntarikon a birnin Bamenda lokacin da ‘yan bindiga suka bude masa wuta, in ji abokin aikinsa Melanie Ndefru.

Wannan ne dan jarida na uku da aka kashe a kasar tun farkon shekarar 2023.

Mai jaridar da Nsoh ke yi wa aiki ya ce dan jaridar ya gama aiki kan jaridar da za ta fito ranar Litinin kenan aka kashe shi.

"Rasuwarsa abin tashin hankali ne," a cewar Tarhyang Enowbikah Tabe, mawallafin jaridar the Advocate.

Kungiyar ‘yan jarida masu amfani da harshen Ingilishi a Jamhuriyar Kamaru (CAMASEJ) ta tabbatar da mutuwar Nsoh, kuma ta nemi a yi bincike don gano wadanda suka kashe shi.

“Wannan hari kan dan jarida babban al'amari ne. Tashin hankalin da aka dade ana yi a arewa maso yammaci da kudu maso yammaci sun saka ‘yan jarida cikin fargaba,” in ji CAMASEJ.

Hukumomi a yankin sun ce ba su da masaniyar game da harin da ya kashe dan jaridar ba, kuma kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin kisan.

A farkon wannan shekarar, an kashe wani mai gabatar da labarai a gidan rediyo da kuma wani dan jarida a hare-hare biyun da aka kai ciki ko kuma kusa da babban birnin kasar Yaounde.

Bamenda ya kasance daya daga cikin biranen da suka fi fuskantar tashin hankali na ‘yan a-waren da ke son ballewa don kafa Jamhuriyar Ambazonia.

An kashe dubban mutane a yakin da ake yi tsakanin dakarun gwamnati da kuma ‘yan a-ware.

TRT Afrika da abokan hulda