Alamuran siyasa sun dauki zafi a Tunisiya/ Hoto: TRT Haber

An gurfanar da shugaban gwagwarmayar Nahda kuma tsohon Shugaban Majalisar Dokoki a Tunisiya, Rashid Al-Gannushi a gaban kotu bayan tsare shi na tsawon sa'a 48.

A lokacin buda-bakin ranar 17 ga Afrilu ne aka kai sumame gidan Al-Gannushi tare da yin awon gaba da shi, bayan amsa tambayoyi a ofishin masu gabatar da kara na tsawon awanni 48, ya gurfana a gaban kotun Tunisiya.

Lauyan Nahda Habib bin Sidhum ya fitar da sanarwa ta shafin sada zumunta cewa an kama Al-Gannushi tare da karin wasu mutum 11 bisa tuhumar su da ‘kitsa kitimirmira ga tsaron kasa’.

Daga cikin jagororin Nahda da aka kama tare da Al-Gannushi har da Muhammad Al-Kumani da Bilkasim Hasan.

Bayan kama Al-Gannushi, kungiyar Nahda ta fitar da rubutacciyar sanarwa inda ta yi kira ga dukkan ‘yan adawa da su hada kai waje guda don magance dauki dai-dai da take hakki da ‘yancinsu da ake yi a Tunisiya.

Sanarwar ta kara da cewa kama Al-Gannushi na da matukar hatsari , kuma suna kira da a saki shugaban na Nahda ba tare da bata lokaci ba.

Har yanzu babu wata sanarwa da gwamnatin Tunisiya ta fitar kan laifukan da ake zargin Al-Gannushi da aikatawa.

TRT Afrika da abokan hulda