An gargadi sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar su guji yi wa Mohamed Bazoum illa

An gargadi sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar su guji yi wa Mohamed Bazoum illa

Jamus ta ce sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar za su dandana kudarsu idan wani abu mara kyau ya samu Mohamed Bazoum.
Mohamed Bazoum ya ce sojojin da suka yi juyin mulkin sun yi garkuwa da shi yana mai yin kira ga kasashe irin su Amurka su kai masa dauki./Hoto: Shafin Facebook na Mohamed Bazoum

Gwamnatin Jamus ta gargadi sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar su guji ya yi Shugaba Mohamed Bazoum illa.

A yayin da yake magana da manema labarai a birnin Berlin ranar Litinin, kakakin Ma'aikatar Wajen kasar Sebastian Fischer ya bayyana karara cewa sun damu da halin da Bazoum yake ciki.

"Hakan ne ya sa nake son yin amfani da wannan dama na kara aikewa da sako ga sojojin da suka yi juyin mulki cewa za su dandana kudarsu idan wani abu ya faru da zababben shugaba Bazoum da iyalansa," in ji Fischer.

Ya ce za su kakaba takunkumai da gurfanar da sojojin a kotun duniya idan wani abu marasa kyau ya samu hambararren shugaban na Nijar.

A makon jiya, Mohamed Bazoum ya rubuta wata wasika da aka wallafa a jaridar Washington Post inda ya ce sojojin na Nijar sun yi garkuwa da shi.

Ya nemi taimakon kasashen duniya irin su Amurka wajen ganin sun ceto kasar daga hannun sojojin da suka kifar da gwamnatinsa.

Sake nazari

A gefe guda, kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka ta ce za ta gudanar da taro ranar Alhamis kan matakin da za ta dauka bayan wa'adin da ta bai wa sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar ya kare.

Kungiyar ta bayyana haka ne a sanarwar da ta fitar ranar Litinin, kwana guda bayan wa'adin da ta bai wa sojojin su mayar da Mohamed Bazoum kan mulki ya kare.

Sanarwar, wadda kakakin kungiyar Emos Lungu ya fitar ta ce "shugabannin ECOWAS za su yi nazari da tattaunawa game da halin siyasa da abubuwan da ke faruwa a baya bayan nan a Nijar."

Kungiyar ta fitar da sanarwar ce a yayin da Mali da Burkina Faso suka ce za su tura wakilai Jamhuriyar Nijar domin nuna goyon baya ga sojojin da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum.

"Burkina Faso da Mali za su tura wakilai Yamai," a cewar rundunar sojin Mali. "Manufar hakan ita ce mu muna goyon bayan mu kasashe biyu ga 'yar uwarmu Nijar."

Sojojin da suka yi juyin mulkin sun yi watsi da wa'adin da ECOWAS ta ba su na mako guda domin su mayar da Bazoum kan mulki ko su fuskanci karfin soji.

Amma Mali da Burkina Faso, kasashen da sojoji suka karbe iko a 2020 da 2022, sun yi gargadin cewa za su dauki hakan a matsayin takalarsu yaki.

A yayin da wa'adin ya kare, sojojin sun rufe sararin samaniyar kasar bayan da suka yi zargin cewa dakarun ECOWAS na barazanar kai musu hari.

A makon jiya, manyan hafsoshin tsaron kasashen kungiyar ECOWAS sun fitar da tsarin da za su bi wajen kai hari da kuma lokacin da za su kai shi Jamhuriyar, idan sojojin ba su saki ko mayar da Mohamed Bazoum kan mulki ba.

TRT Afrika da abokan hulda