An fara bikin ne a makon jiya, sai dai an dakatar shi bayan tarzomar da ta ɓarke a Ibadan. Hoto: Kolawole Aliyu

Rundunar ‘yan sandan Oyo da ke kudancin Nijeriya ta yi gargadi kan ta da hankulan jama'a a yayin bikin Egungun na shekara-shekara da ake gudanarwa a jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Adewale Osifeso ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Ibadan, inda ya bayyana wasu tsare-tsare na tabbatar da zaman lafiya a lokacin gudanar da bikin a bana.

A sanarwar da TRT Afrika ta samu, jami’in ya ce rundunar ta kammala shirye-shiryen tabbatar da tsaro ga mazauna yankin da kuma ’yan kasa nagari.

An fara bikin ne a makon jiya, sai dai an dakatar shi bayan tarzomar da ta ɓarke a Ibadan.

Amma a yanzu rundunar ‘yan sanda ta fitar da sanarwar gargadin bayan da Sarkin Ibadan ya ba da sanarwar cewa za a ci gaba da gudanar da bikin.

Sanarwar ta ce “Daga ranar Litinin din nan, tsarin tsaro na rundunar 'yan sanda zai karkata gaba daya wajen tabbatar da doka da oda a mataki na gaba na jerin bikin Dodannin Egungun da kuma bayansa.

"Kwamishinan 'yan sanda na jihar Oyo, CP Adebola Hamzat, ya ba da umarnin aikewa da jami'an hukumar cikin gaggawa tare da samar da bayanan sirri, da dabaru don samun nasarar taron bakin," in ji SP Osifeso.

Ya kara da cewa mazauna jihar za su shaida yadda za a gudanar da sintiri, da binciken karkashin kasa da leken asiri, da kuma ayyukan sa ido na ingantacciyar fasahar zamani a yayin da ake shirye-shiryen bikin.

Ya kuma bukaci iyaye da shugabannin al’umma da su rika bai wa ‘ya’yansu shawarar ka da masu laifi su yi amfani da su wajen hargitsa ko ta da tarzoma a yayin jerin gwano na bikin.

SP Osifeso ya ce rundunar za ta sa kafar wando daya da duk wani mai shirin yin barazana ga zaman lafiyar jama'a a lokacin bikin Dodannin na Egungun.

A kwanakin baya ne babban basaraken lardin Ibadan, Olubadan na Ibadan, Oba Lekan Balogun, ya dage dakatarwar da aka yi na bikin Dodannin Egungun.

Ci gaba da biki

Tun da farko dai an dakatar da bikin ne sakamakon tashe-tashen hankula da aka samu a makon da ya gabata a wurare daban-daban har da cikin birnin Ibadan.

Matakin janye dakatar da bikin na kunshe ne a cikin wata sanarwar da aka raba wa manema labarai a Ibadan ranar Juma’ar da ta gabata ta hannun mai taimaka wa babban basaraken a bangaren watsa labarai Oladele Ogunsola.

Sanarwar ta bayyana cewa an dage dakatarwar ne bayan da aka yi sulhu tsakanin fadar Olubadan da shugabannin masu bauta na Dodannin Egungun da ake kira Alaagbaas a lardin.

Haramcin shiga bikin

Sanarwar ta kara da cewa, Mai martaba Sarkin sarakuna na lardin Ibadan ba zai lamunci duk wani nau'i na "tarzoma ko tashin hankali a yayin bikin da kuma a kowane lokaci ba."

Olubadan ya dauki tsattsauran matakin ne sakamakon tashe-tashen hankula, sai dai a yanzu ya yi sassauci ga mabiyansa bisa la'akari da muhimmancin bikin tare da gargadin cewa duk wanda aka samu yana haddasa fitina zai fuskanci haramcin shiga a dama da shi a bikin gaba daya.

Tun a baya dai Alaagbaas sun roki Olubadan da ya yi afuwa, inda suka dage cewa babu wani tashin hankalin da ya faru a sakamakon hamayya tsakanin masu bautar doddanin Egungun da ke adawa da juna.

Sun yi zargin cewa wasu bata-gari ne suka haddasa rikicin, inda suka fake da bikin suna kai farmaki kan jama'ar da ba su ji ba ba su gani ba, tare da wawashe kayayyakin jama'a.

Al'ummar Yarbawa da ke zaune a kudu maso yammacin Najeria sun yi imanin cewa Dodannin Egungun wakilai ne na matattun kakanninsu wadanda suka dawo don su rayu, su kuma taimaka wa jama'arsu.

Mabiya addinin gargajiya a garuruwan Yarbawa sun yi imanin cewa addu’o’in Dodannin Egungun da suke yi masu na karbuwa a lokacin da suke bauta wa Dodaddin na Egungun, a lokacin da suke kiran ruhun kakanninsu.

TRT Afrika