Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Nijeriya ta ja hankalin ‘yan ƙasar kan ɓullar wata gurbatacciyar allura ta Giga-S da aka gano a garin Aba da ke jihar Abia a kudancin ƙasar.
A sanarwar da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet a ranar Litinin, NAFDAC ta ce an fara gano gurbatacciyar allurar, wadda ake amfani da ita don maganin tsananin cututtukan infection, a wani shago da ke Kasuwar Araria a Aba.
Ana amfani da allurar Giga–S mai ɗauke da sinadaran Ceftriaxone + Sulbactam ne don magance cututtuka irin su septicemia da numoniya da kuma sanƙarau.
Sai dai duk da cewa a jihar Abia kawai aka gano gurɓatacciyar allurar zuwa yanzu, NAFDAC ta ƙara ce “akwai yiwuwar ta yaɗu a wasu sassan ƙasar ta hanyar kasuwannin bayan-fage.
“Don haka yana da muhimmanci sosai a gano ta a kuma tabbatar an kawar da ita daga yaɗuwa don gudun cutar da marasa lafiya.”
NAFDAC ta ja hankalin masu shigar da kaya da ‘yan kasuwa da ma’aikatan lafiya da su yi taka tsantsan wajen samar da magunguna don gudun kada a ci karo da allurar.
Ta ce yana da muhimmanci a tabbatar da cewa duk magungunan da za a saya sun fito ne daga hannun ingantattun kamfanoni.
NAFDAC ta shawarci duk waɗanda suka san suna da wannan gurɓatacciyar allura a hannunsu da su daina sayar da ita ko amfani da ita sannan su miƙa ta ga ofishinta mafi kusa.
“Idan kana da wannan gurɓatacciyar (allura), kar ku yi amfani da ita, Idan ka yi amfani da ita ko ka san wanda ya yi amfani da ita sannan ya shiga wani hali to muna shawartarku da ku yi gaggawar kai shi asibiti,” hukumar ta ƙara da cewa.