An gano wani yaro dan shekara bakwai a raye bayan ya bata tsawon kwanaki biyar a wani wurin ajiyar zakuna da namun daji a arewacin Zimbabwe, in ji hukumar namun daji a ranar Juma'a.
Yaron ya yi ta yawo a cikin gandun dajin Matusadona da ke kusa da kauyensu a ranar 27 ga watan Disamba, kuma an same shi bayan kwanaki biyar, a nisan tazarar kilomita 50 (kimanin mil 30), in ji kakakin ZimParks Tinashe Farawo.
Ya rayu ne yana cin ‘ya’yan itatuwa da ruwa ta hanyar tono a wani bakin kogi, dabarar da ta shahara a yankunan da ke fama da fari a Zimbabwe, in ji Farawo a cikin wata sanarwa.
“Abin mamaki, an yi kiyasin cewa ya bi ta dajin dajin Matusadona mai tazarar kilomita 49 daga kauyensu har inda aka same shi,” in ji Farawo.
An gano takun sawunsa
Masu kula da gandun daji da ‘yan sanda sun kaddamar da neman yaron nan take bayan samun labarin cewa ya ba a gan shi ba amma mamakon ruwan sama da aka yi ta yi ta hana su kai wa ga ci.
An bi takun sawunsa a ranar 30 ga Disamba lamarin da ya kai ga gano yaron mai suna Tinotenda Pundu, da safiyar washegari, in ji shi.
An kwantar da yaron a asibiti saboda ya galabaita sosai amma ba a ga wani rauni a jikinsa ba, in ji wata 'yar majalisa Mutsa Murombedzi da ta fito daga yankin. "Tsirar tasa abin mamaki ne ƙwarai," kamar yadda ta shaida wa AFP.
“Amma yana da wayo tun da har ya gano zai iya kwana a kan duwatsun da ke yankin ta yadda zakuna da sauran namun daji ba za su iya cim ma ba."
'Buga ganga'
"Mutanen ƙauyen sun taimaka wajen neman yaron, inda suka dinga buga ganguna da fatan zai jiyo sautin," in ji 'yar majalisar. Amma an same shi ne kawai tare da taimakon jami’an tsaro da suka iya shiga cikin dajin domin nemansa.
Gidan gandun dajin na Matusadona da ke kusa da tafkin Kariba na kasar Zimbabwe yana dauke da namun daji da suka hada da zakuna da damisa da giwaye da kuma ɓauna kamar yadda shafin intanet na gandun dajin ya bayyana.