Akalla mutane 800,000 ne aka kashe a yayin tashin hankalin kasar Rwanda. / Hoto: AP      

An gano gawarwakin mutane 119 da ake kyautata zaton sun mutu a kisan kiyashin da aka yi a yankin kudancin kasar Rwanda a shekarar 1994, kamar yadda wani jami'i a kasar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press.

An gano kaburburan ne a ranar Alhamis, kusan shekaru 30 bayan aukuwar wani kazamin rikici na kabilanci da ya yi sanadiyar mutuwar ‘yan kabilar Tusti akalla 800,000 da tsirarrun ‘yan Hutu daga 'yan tawayen Hutu tsakanin ranar 7 ga watan Afrilu zuwa 15 ga Yulin shekarar 1994.

"Ana ci gaba da gano wasu karin gawarwakin wandanda aka kashe saboda wadanda suka aikata kisan kiyashin sun yi iyakacin kokarinsu wajen boye bayanan da iya tona asirinsu," a cewar Naphtal Ahishakiye, babban sakatare na kungiyar wadanda suka tsira daga kisan kare dangi na Ibuka.

A watan Oktoba ne hukumomi suka fara gano wasu gawawwaki guda shida a kasan wani gida da ake ginawa a gundumar Huye.

An gano karin wasu gawarwakin bayan ci gaba da bincike da ake yi.

Louise Uwimana, wacce ta tsira daga kisan kiyashin kana mazauniya a gundumar Huye, ta ce ta yi matukar bakin ciki da ta samu labarin cewa makwabtanta sun boye bayanai game da kaburburan a daidai lokacin da gwamnati ke karfafa sulhu.

A watan Afrilu ne kasar Rwanda za ta gudanar da gagarumin bikin cika shekaru 30 da kisan kiyashin da ya faru a kasar, inda za a ajiye furanni a kan kaburbura.

TRT Afrika