Rundunar sojin Nijeriya da 'yan sa kai da sauran hukumomin tsaro suna ci gaba da aikin ceton mutanen da suka maƙale a cikin ambaliyar ruwa suna kai su wuraren da ke da aminci.
Mummunar ambaliyar ta ti sanadin aƙalla rayukan mutum 30 da kuma raba mutum 400,000 da muhallansu, kamar yadda jami'ai suka faɗa a ranar Laraba.
Mai magana da yawun hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA, Ezekiel Manzo ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa "Mutum 30 ne suka mutum."
Ita ma shugabar hukumar NEMA Zubaida Umar ta ce "Al'amarin Maiduguri yana da ban tsoro." “Ambaliya ta mamaye kusan kashi 40 cikin 100 na daukacin birnin, an tilasta wa mutane barin gidajensu kuma sun bazu ko ina.
Da ya ziyarci yankunan da lamarin ya fi ƙamari a Maiduguri, Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya zagaya yankin unguwar Custom inda gidan yarin yake.
Yayin da ake rangadin, ana kwashe gawarwakin mutane. Hakazalika sojoji da jami'an tsaro da masu aikin sa kai na farar hula suna kwashe mutanen da suka maƙale.
Duk da cewa ruwan ya fara janyewa a wasu wuraren da ambaliyar ruwa ta mamaye a Maiduguri, yankunan da abin ya fi ƙamari kamar su Kasuwar Gamboru da Kasuwan Shanu da Custom Area da Fori, da Abbaganaram har yanzu a malale suke.
Aikin ceto
A cewar NEMA, sama da gidaje 23,000, da mutum 150,000 ne suka fuskanci bala'in ambaliyar ruwan.
“Mun kuma aike da dakunan shan magani na tafi da gidanka da kayayyakin jinya tare da likitocin asibitin sojoji domin kula da ‘yan gudun hijirar da ke sansanoni da ke bukatar kula da lafiya,” in ji Zubaida.
“Hakan yana da muhimmanci domin babban asibitin Maiduguri shi ma ambaliyar ya shafe shi. Mun samar da kwale-kwale da masunta da ke shiga cikin al’ummomin da ambaliyar ruwa ta mamaye tare da kubutar da mutanen da suka makale.”
Ta kara da cewa, “Mun tura tankunanmu na ruwa domin samar da ruwan sha mai tsafta saboda mun damu da yiwuwar barkewar cututtuka masu yaduwa.”