An daure Ministar gwamnatin Uganda a kurkuku a lamarin da ba a saba gani na rashawa da ya shafi manyan jami’ai, inda ake zargin ta da sama da fadi da kwanukan rufi da aka tanada don gidajen masu karamin karfi a yankin Karamoja na arewacin kasar.
An tuhumi Mary Goretti Kitutu, Ministar Kula da Harkokin Karamoja da dan uwanta Michael Naboya Kitutu bisa damfarar gwamnati.
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Uganda ta bayyana cewa ana tuhumar ‘yan uwan biyu da hada baki a damfarar gwamnati wajen sama da fadi da kayan da aka sayo don amfanin mutane marasa galihu a yankin Karamoja.
Sanarwar da Hukumar ta fitar ta kara da cewa an tsare ministar a kurkuku har nan da ranar 12 ga Afrilu.
A ranar Alhamis din nan ne Minista Mary Goretti Kitutu da dan uwanta suka gurfana a gaban Kotun Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Uganda.
An sayo kwanukan rufin don amfani da su wajen gina gidajen masu karamin karfi a yankin Karamoja, yankin da ke fama da rashin cigaba, kuma yake fama da matsaloli a arewa maso-yammacin Uganda kusa da iyakar kasashen Kenya da Sudan ta Kudu.
Wannan abun kunya ya janyo ce-ce-ku-ce da kokawar jama’a da dama a kasar da cin hanci da rashawa suka yi wa gwamnatinta katutu.
Abu ne da ba a saba gani ba na gurfanar da babban mai rike da mukamin siyasa saboda zargin cin hanci da rashawa, kuma Kitutu ce jami'a mafi girman mukami da aka gurfanar a gaban kotu a ‘yan shekarun nan.
Abu mai kama da wannan da ya faru shi ne na 2007, lokacin da aka tuhumi wasu jami’an gwamnati biyu; Jim Muhwezi da Mike Mukula da sama da fadin miliyoyin daloli na bayar da agaji.
Madugun ‘yan adawar Uganda Bobi Wine ya ce tuhumar Kitutu ‘Da walakin ne’, ya kuma zargi gwamnatin Yoweri Museveni da zama mafi muni wajen aikata cin hanci da rashawa.
Mawakin da ya zama dan takarar shugaban kasa ya ce “Kamata ya yi dukkan mambobin gwamnatin Museveni da shi kansa su kasance a cikin kurkuku saboda cin hanci da rashawa”.
Ya kara da cewa “ba za mu yi murnar tuhuma kan kwanon rufi ba a lokacin da ake almabazzaranci da biliyoyin daloli.”