An yanke wa maidakin hambararren shugaban kasar Gabon, Ali Bongo Ondimba, hukuncin zaman gidan kaso. Lauyanta ya fada cewa an yi wa Sylvia Odimba Valentin daurin talala tun lokacin da aka yi wa maigidanta juyin mulki, a karshen watan Agusta.
Lauyan mai suna Francois Zimeray, ya fada wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an zargi Sylvia Bongo Ondimba Valentin da almubazzaranci da kudin jama'a, inda aka yanke mata hukunci ranar Laraba. Sai dai ya soki hukuncin da cewa, "na son-rai ne... kuma ya saba wa doka".
An tuhumi maidakin Ali Bongo ranar 28 ga watan Satumba da zargin halatta kudin haram, da zamba, da kirkirar takardun bogi.
Sylvia Bongo ta kasance karkashin daurin talala, a babban birnin kasar, Libreville, tun juyin mulkin ranar 30 ga watan Agusta wanda ya kawo karshen shekaru 55 na mulkin gidan Bongo.
Sauya sakamakon zabe
Sojin da suka hambarar da gwamnatin sun yi zargin cewa tsohon shugaban, tare da hadin bakin mukarrabansa sun sauya sakamakon zaben kasar.
Sun zargi Sylvia Bongo da danta, Nourredin Bongo Valentin, da yaudarar tsohon shugaban, wanda bai warke daga ciwon shanyewar barin jiki da ta same shi ba a shekarar 2018.
An tuhumi mutanen biyu da jagorancin kasar ta bayan-fage, tsawon shekaru biyar da suka gabata, tare da ɓarnata dukiyar al'umma.
Shi ma dan nata, Nourredin Bongo Valentin an masa daurin talala tun bayan juyin mulkin, kuma aka tuhume shi da rashawa.
Lauya Zimeray ya ce, "Muna Allah wadai da wannan mataki da ya saɓa wa doka".
Hamɓarar da Bongo
"Akwai bambanci tsakanin adalci da yin abubuwa ba bisa ka'ida ba, wanda yake tsakanin kin bin doka da kuma daukar fansa", in ji Zimeray.
Mai shigar da kara na gwamnati bai mai da martani kan tambayar da AFP ya tura masa ba, ya zuwa yanzu.
Sojojin kasar sun hambarar da Ali Bongo, dan shekara 64, wanda ya mulki kasar da ke tsakiyar Afirka tun shekarar 2009, bayan da aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa.
Da yawan mutane sun kalli wannan abu a matsayin 'yantar da kasar, maimakon juyin mulkin soji.
An zabi Ali Bongo a matsayin shugaban kasa bayan da mahaifinsa Omar Bongo ya rasu a 2009, bayan mulkar kasar kusan shekaru 42.
A Afirka, Gabon ita ce kasa ta uku da ta fi arziki bisa ma'aunin GDP, amma kuma mutum daya cikin uku na 'yan kasar yana rayuwa cikin da'irar talauci, a cewar Bankin Duniya.