Tun da fari Kwamishinan 'yansan jihar Usaini Gumel ne ya sanar da sanya dokar ranar Laraba. Hoto: Kano Police

Rundunar 'yan sandan Jihar Kano da ke arewa maso yammacin Nijeriya ta sanar da dage dokar takaita zirga-zirga da ta sanya ranar Laraba, bayan yanke hukunci kan kujerar gwamnan jihar da kotu ta yi.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Abdullahi Kiyawa ne ya wallafa sanarwar a shafinsa na Facebook ranar Alhamis da yamma, inda ya ce gwamnatin jihar ce ta ba da umarnin ɗage dokar.

A ranar Laraba ne kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke hukunci inda ta soke Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ayyana Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya ci zaben, a cikin wani yanayi na tsaurara tsaro, inda jim kadan bayan hukuncin aka saka dokar hana fita ta awa 24 a fadin jihar don dakile duk wata barazana ta tsaro.

Yanke hukuncin ya sa an soma zaman dar-dar a fadin jihar domin tsoron abin da ka je ya komo.

Rahotanni daga Kano sun ce mutane sun mutunta dokar ta yadda tun daga yammacin Laraba har yinin Alhamis tituna suka kasance fayau, kuma zirga-zirga ta takaita.

Rundunar 'yan sandan ta ce ta jibge jami'an tsaro a ko'ina ciki har da hanyoyin shiga da kuma fita daga jihar ta Kano domin dakile duk wata barazana ta tsaro.

Sai dai ta kara da cewa an bar masu ayyukan gaggawa irin su likitoci da 'yan kwana-kwana da makamantansu su yi zirga-zirga.

TRT Afrika