Hukumar NIDCOM ta ce ‘yan matan na bayar da bayanai masu amfani da nufin zakulo waɗanda suka yi safarar su inda suka ce an yaudare su an jefa su cikin karuwanci. / Hoto: NIDCOM

Gwamnatin Nijeriya ta sanar da ceto mata ‘yan ƙasar 13 a cikin mako guda waɗanda aka yi safarar su zuwa Ghana.

Shugabar Hukumar da ke Kula da ‘Yan Nijeriya Mazauna Waje Abike Dabiri-Erewa ce ta sanar da hakan a ranar Talata.

Ta bayyana cewa ƙasa da mako guda bayan ceto mata 11 waɗanda aka kai ƙasar ta Ghana, a ranar Litinin ɗin nan an sake ceto wasu biyu wanda hakan ya sa suka zama 13.

Haka kuma ta bayyana cewa an ceto matan ne da taimakon ƙungiyar ‘yan Nijeriya mazauna waje ƙarƙashin jagorancin Cif Calistus.

Dabiri ta sake nanata kiran ta na a hada karfi da karfe wajen yaki da safarar mutane ta kowane fanni domin a cewarta wani nau'i ne na bauta a zamanance.

Ta ce ‘yan matan na bayar da bayanai masu amfani da nufin zakulo waɗanda suka yi safarar su inda suka ce an yaudare su an jefa su cikin karuwanci.

Ta kara da cewa za a yi shirin mayar da su Nijeriya da kuma mika su ga hukumar NAPTIP.

Matan biyu na baya-bayayn nan da aka ceto a Legas suke zama, ɗaya asalin ‘yar Edo ce ɗaya kuma ‘yar Legas.

Sai kuma matan 11 da aka ceto a farkon mako suna tsakanin shekaru 15 ne zuwa 16 waɗanda asalinsu ‘yan jihohin Imo ne da Filato inda aka yaudare su aka kai su Ghana da sunan za su rinƙa sayar da kaya a shago inda daga baya aka saka su karuwanci.

TRT Afrika