'Yan bindiga da ke ikirarin jihadi sun kashe sojojin Nijar ashirin da tara a wani hari da suka kai musu a kan iyakar kasar da Mali, kamar yadda ma'aikatar tsaron kasar ta bayyana ranar Litinin da daddare.
Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar wadda aka karanta a gidan talbijin na kasar ta ce 'yan ta'adda fiye da dari sun yi amfani da "abubuwan fashewa da motoci masu harba makamai masu linzami" wajen kai hari kan sojojin.
Sojoji biyu sun ji munanan raunuka kuma an "kashe gomman 'yan ta'adda", in ji sanarwar.
Rundunar sojin kasar ta ayyana zaman makokin kwana uku bayan faruwar lamarin.
Lamarin ya faru ne a yayin da sojojin suke kai farmaki da zummar "murkushe barazanar da 'yan kungiyar Islamic State" suke yi a yankin, a cewar ma'aikatar tsaron Nijar.
"An saurari hirarrakin da 'yan ta'addar suke yi ta waya, kuma an tilasta musu janyewa daga yankin", a cewar ma'aikatar tsaron, tana mai karawa da cewa maharan sun samu tallafin "kwararru na kasashen waje" ko da yake ba ta yi karin haske kan abin da take nufi ba.
Labari mai alaka: Sojojin Nijar sun kashe 'yan ta'adda 55 a yankin Tafkin Chadi
Yankin Sahel ya kwashe fiye da shekara goma yana fama da hare-haren 'yan ta'adda, wanda aka fara a Mali a 2012 kuma ya watsu zuwa makwabta wato Nijar da Burkina Faso a 2015.
'Yan ta'adda da ke da alaka da Islamic State da Al-Qaeda suna yawan kai hare-hare a yankunan da ke kan iyakar Nijar, Mali da Burkina Faso.
Irin wadannan hare-hare ne suka sa sojoji suka yi juyin mulki a kasashen uku, na baya-bayan nan shi ne na Jamhuriyar Nijar inda sojoji suka kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum a watan Yulin da ya gabata.
A watan Agusta, masu ikirarin jihadi sun kashe akalla sojoji 17 na Nijar sannan suka jikkata kusan 20 a harin da suka kai garuruwan da ke kan iyakar kasar da Burkina Faso.