Gabanin zaman Majalisar Dokokin Ghana a ranar Talata, sashen tsaro na majalisar ya ɗauki ƙarin matakai domin tabbatar da tsaro a babban ɗakin taro na Accra wato AICC wanda a nan ne majalisar ke gudanar da zamanta na wucin-gadi.
Hakan na faruwa ne bayan umarnin da Kotun Ƙolin Ghana ta bayar na soke matakin da Kakakin Majalisar Dokokin Ghana ya ɗauka na ayyana cewa ‘yan majalisa huɗu sun rasa kujerunsu sakamakon sauya sheƙa da suka yi.
A wata sanarwa da Wing Commander Fredrick Bawa mai ritaya, mataimakin shugaban tsaro na majalisar, ya fitar ya ce an ɗauki matakan tabbatar da tsaro da kariya ga kakakin majalisa da mambobin majalisar da sauran ma’aikatan majalisar.
Sanarwar ta buƙaci ‘yan majalisar da sauran ma’aikata da ‘yan jarida su bayar da haɗin kai saboda za a gudanar da bincike mai tsauri kafin shiga zauren majalisar.
Sanarwar ta ƙara da cewa ba za a bar jami’an da ke tsaron lafiyar ‘yan majalisar su shiga zauren majalisar ba.
Haka kuma ta ce ba za a amince a ajiye motoci a kusa da wurin da majalisar ke gudanar da zaman nata ba.
A cewar sanarwar, akwai wuri na musamman da aka tanada a kusa da zauren majalisar na wucin-gadi wanda motoci za su ajiye mambobin majalisar, haka kuma ‘yan sandan Ghana su za su nuna wurin da za a rinƙa ajiye mota.
An kuma buƙaci ‘yan majalisar su rataya katinsu na ‘yan majalisa a wuya kafin shiga majalisar, inda za a buɗe ƙofar shiga majalisar da misalin ƙarfe takwas na safe.
Sanarwar ta kuma ƙara da cewa ba za a bai wa sauran jama’ar gari damar shiga majalisar ba.