Amurka ta sanar da kakaba takunkumi na farko kan bangarori biyu da ke rikici da juna a Sudan a ranar Alhamis, bayan rashin mutunta tattaunawa da aka yi ta yi tsakanin dakarun sojin biyu.
Hakan kuma na zuwa ne kasa da wata guda bayan sanya hannu da Shugaba Joe Biden kan wata doka ta zartar da takunkumi ga wadanda ke barazana ga "zaman lafiya da tsaro" a Sudan.
"A yau, muna bin diddigin takunkuman da aka sanya kan karya tattalin arziki da hana biza ga wadanda ke da hannu wajen ta da zaune tsaye a Sudan da kuma fitar da sabbin shawarwari kan harkokin kasuwanci na kasar," a cewar sanarwar da mai ba da shawara kan harkokin tsaro na Amurka Jake Sullivan ya fitar.
Ya kara da cewa: “Al'ummar Sudan ba su nemi wannan yaki ba, Amurka za ta ci gaba da kasancewa tare da su, za mu ci gaba da goyon bayan bukatarsu ta neman mika mulki ga tsarin dimokuradiyya.
Takunkumin ya shafi mutanen da ke da alaka da dakarun sojin Sudan da dakarun rundunar Rapid Support Forces RSF da kuma tsoffin shugabannin da suka dade a gwamnatin Omar al-Bashir.
Haka kuma Ma'aikatar Baitulmali Amurka ta kakaba takunkumi kan kamfanoni hudu a Sudan da ake zargi suna taimaka wa sojojin kasar da RSF.
Kamfanonin sun hada da Defence Industries System (DIS), da babbar masana’antar soji ta Sudan da aka kiyasta kudin shigar da take samu ya kai dala kusan biliyan 2, da kuma Sudan Master Technology, wani kamfanin makamai da ke da hannun jari a wasu rassan DIS masu yawa.
Yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Saudiyya da Amurka suka taimaka wajen kullawa tsakanin bangarorin biyu ta kare a ranar Litinin.
Manya janar-janar biyun da ke fada da juna sun amince su tsawaita yarjejeniyar tsawon kwanaki biyar, sai dai hakan bai yiwu ba domin sun yi fatali da tattaunawar zaman lafiyar a ranar Laraba.
Sojojin sun yi ikirarin cewa RSF ta gaza mutunta da "duk wasu sharudda da yarjejeniyar tsagaita wuta ta gindaya."