An rantsar da Janar Brice Oligui Nguema a matsayin sabon shugaban kasar Gabon a farkon wannan wata. Hoto: AFP

Amurka ta ce za ta dakatar da taimakon da take ba Gabon bayan da aka yi juyin mulki a kasar a watan jiya.

"Gwamnatin kasar Amurka ta dakatar da wasu shirye-shiryen tallafi ga gwamnatin Gabon yayin da muke nazari kan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar," kamar yadda Sakataren Harkokin Wajen Kasar Antony Blinken ya bayyana a wata sanarwa ranar Talata.

Ya ce Amurka za ta ci gaba da harkokin diflomasiyya da aikace-aikacen ofishin jakadanci a kasar Gabon wacce take da arzikin man fetur kuma kasar tana shiyyar Tsakiyar Afirka ne.

Matakin na dan lokaci ne yayin da ma'aikatar harkokin wajen Amurka take kokarin daukar matsaya kan juyin mulkin da sojoji suka yi a Gabon, wanda karkashin dokar Amurka za a datse tallafin da ake ba kasar ne.

Kayyade taimako

Tun da farko jami'ai a Amurka sun ce taimakon da kasar take ba Gabon a kayyade yake, iyalan Bongo sun kwashe fiye da shekara 50 suna mulkin kasar.

Amurka tana taimaka wa Nijar ta fuskar soji da tattalin arziki, ita ma wata kasar Afirka ce da sojoji suka yi juyin mulki a baya-bayan nan.

Sojoji a Gabon sun kifar da gwamnatin Ali Bongo Ondimba a ranar 30 ga watan Agusta, jim kadan bayan ya yi ikirarin lashe zabe wanda yake tattare da matsaloli.

Sojojin sun nada jagoran 'yan adawa Raymond Ndong Sima a matsayin firai minista, wanda yayin da yake jawabi ga Majalisar Dinkin Duniya a makon jiya ya yi alkawarin yin sabon zabe kuma ya bukaci kada Kasashen Yamma su yi Allah wadai da juyin mulkin.

TRT Afrika