Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou ya yi gargadin cewa yin amfani da karfin soji a kan sojojin kasar zai zama babban kusukure.
Ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta a ranar Asabar.
Tun bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum ranar 26 ga watan Yuli, kungiyar ECOWAS take barazanar yin amfani da karfi soji don dawo da shi kan mulki.
Sai dai Mahamadou Issoufou, wanda shi ne shugaban da ya mika wa Bazoum mulki bayan gudanar da zabe a kasar a 2021, ya ce yin amfani da karfi bai taba samar da mafita kan kowane irin rikici ba.
Ya ce ya yi amanna shugabannin kungiyar ECOWAS za su yi amfani da hikima don warware rikicin siyasar Nijar.
“Har yanzu ina cikin damuwa kan rikicin da kasata Nijar ke ciki, ina kara jaddada cewa tattaunawa ce kadai za ta bude hanyar mayar da dimokuradiyya cikin gaggawa,” in ji Issoufou.
"Amfani da sojoji, wanda tasirin hakan kan bil’adama da kayayyaki ba ya misaltuwa, zai zama wata hanya ta samun rashin zaman lafiya.
“Bayan haka irin wannan bai taba zama ci-gaba ga kowace al’umma ba. Fiye da kuskure, amfani da su zai zama kuskure.
“Ina tabbatar da cewa shugabannin ECOWAS za su yi amfani da hikimarsu domin kada su aikata irin wannan kuskuren,” in ji tsohon shugaban na Nijar.
Mahamadou Issoufou ne ya goya wa Bazoum baya har ya zama shugaban kasa kuma shi ya mika masa mulki.
Haka kuma dan gidan Mahamadou Issoufou wato Mahamane Sani Mahamadou ya samu mukamin ministan man fetur a gwamnatin Bazoum kuma yana daga cikin wadanda sojojin da suka yi juyin mulki suka kama.
Haka kuma tsohon shugaban na Nijar Mahamadou Issoufou shi ya yi wa Janar Abdourahamane Tchiani, babban jami'in sojan da ya jagoranci juyin mulki, karin girma a 2018.
Janar Tchiani ya kasance babban jami’in da ke gadin fadar shugaban Nijar tun daga shekarar 2011 lokacin da Issoufou ke mulki.