Mummunar ambaliyar ruwa ta shafi kusan mutum miliyan 1.4 da raba aƙalla mutum 379,000 da muhallansu, kamar yadda ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya da ke kula da ayyukan jin ƙai ya bayyana a ranar Asabar.
"Kimanin mutum miliyan 1.4 ne ambaliyar ruwa ta shafa a kananan hukumomi 43 da yankin Abyei, inda jihohin Jonglei da Arewacin Bahr el Ghazal suka ƙunshi fiye da kashi 51 cikin 100 na mutanen da lamarin ya shafa." kamar yadda ofishin jin kai na MDD ya bayyana.
Ya kara da cewa sama da mutum 379,000 ne suka rasa matsugunansu a kananan hukumomi 22 da Abyei.
Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta kara da cewa, "A wannan makon, binciken haɗin gwiwa tsakanin gwamanti da kungiyoyi ya gano karin mutum 1,720 da ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a Mangalla, gundumar Juba ta jihar Equatoria ta tsakiya".
Ta ce an samu bullar cutar zazzabin cizon sauro a jihohin Jonglei, Unity, Upper Nile, Bahr el Ghazal ta Arewa, Tsakiyar Equatoria, da yammacin Equatoria, lamarin da ya jawo babbanr matsala ga tsarin kiwon lafiya tare da ta'azzara cutar a yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa.
“Sakamakon ruwa ya shanye hanyoyi, ayyukan jin kai na fuskantar cikas a daidai lokacin da ma’aikata ke ƙoƙarin kaiwa ga al’ummomin da ke cikin matsala,” kamar yadda ta bayyana.
Wannan ne karo na farko a tsawon gomman shekaru da aka samu ruwan sama mai yawa da mummunar ambaliya da suka yi ɓarna sosai a ƙasar da ke gabashin Afirka.