Shugaban na SEMA ya ce gidaje 7,800 sun rushe sannan ambaliyar ruwan ta lalata kadada 10,337. /Hoto:Ministry of Special Duties, Miga

Hukumomi a Nijeriya sun ce ambaliya sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ta kashe aƙalla mutum 33 a jihar Jigawa.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar (SEMA), Haruna Mairinga, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu ranar Juma'a cewa ruwan da aka kwashe makon nan ana yi a faɗin jihar ya lalata gadoji da rusa gidaje da haddasa ambaliya.

"Mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwan da aka yi a ƙananan hukumomi 14 na jihar nan yanzu sun kai 33 daga 28 da aka tabbatar da mutuwarsu a farkon makon nan," in ji shi.

Ya ƙara da cewa: “Ambaliyar ruwan ta raba aƙalla mutum 44,000 daga muhallansu.”

Shugaban na SEMA ya ce gidaje 7,800 sun rushe sannan ambaliyar ruwan ta lalata kadada 10,337.

A cewarsa dubban mutanen da ambaliyar ruwan ta kora daga gidajensu suna karɓar taimakon abinci da magunguna a matsugunan wucin-gadi da gwamnati ta samar musu.

AA