Ana fargaba game da wadatuwar abinci a ƙasar sakamakon yadda ambaliyar ta yi wa amfanin gona ɓarna. / Hoto: TRT

Aƙalla mutum 170 ambaliyar ruwa ta kashe a Nijeriya sannan kusan mutum 2,000 suka jikkata a cikin mako biyu.

Cibiyar da ke bayar da agajin gaggawa game da ambaliya a Nijeriya NEOC ce ta tabbatar da hakan a ranar Talata inda ta ce ambaliyar ta raba sama da mutum 205,000 da muhallansu.

Kamar yadda alƙaluman da NEOC ɗin ta fitar a ranar Talata, waɗanda hukumar NEMA ta wallafa, zuwa yanzu aƙalla mutum 170 ne suka rasu sannan mutum 1,941 suka jikkata, haka kuma 205,338 suka rasa muhallansu daga duka jihohin Nijeriya.

Jihohi takwas da ke arewacin Nijeriya sun fuskanci mamakon ruwan sama, inda su ma wasu sassan ƙasar ke ci gaba da samun ruwan saman.

Hukumar da ke hasashen yanayi ta Nijeriyar ta sanar da cewa za a ci gaba da samun ruwan sama har zuwa wata mai zuwa.

Haka kuma ambaliyar ta shafe gonaki inda ta lalata amfanin gona a dubban kadadar, wanda hakan ya ƙara saka damuwa dangane da yanayin yadda za ta kasance dangane da batun abinci a ƙasar da ke Yammacin Afirka a bana.

Ahmed Saleh, wani manomi a Jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Nijeriya ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa akasarin manoma sun damu dangane da tasirin ɓarnar da ambaliya ta yi wa gonakinsu kan wadatar abinci a Nijeriya.

Ezekiel Manzo, wanda mai magana da yawun hukumar NEMA ne a Nijeriya, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa tuni suka soma sa ido domin daƙile ambaliyar ruwa ta hanyar haɗa hannu da ma’aikatan hukumomin bayar da agaji na jihohi.

AA