Wani mutum yana ƙetara ruwa a Port Sudan, Sudan, ranar 26 ga watan Agusta, 2024./Hoto:Reuters

Mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa bayan wani dam ya ɓalle yayin da ake mamakon ruwan sama a Sudan sun kai 132, kamar yadda hukumomi suka bayyana ranar Litinin.

Wani kwamitin bayar da agajin gaggawa da gwamnati ta kafa ya ce mutanen da suka mutu a larduna 10 na ƙasar sun kai 132, sannan iyalan da lamarin ya shafa sun haura 31,666 sannan ambaliyar ruwanta shafi ɗaiɗaikun jama'a da suka kai 129,650.

Ya ƙara da cewa ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya rusa gidaje aƙalla 12,420 baki ɗaya sannan ya lalata gida 11,472.

Ruwan saman da aka riƙa sheƙawa ranar Asabar ya janyo ambaliya a yankin Arbat da ke arewacin birnin Port Sudan wanda ke gaɓar Bahar Maliya, lamarin da ya sa madatsar ruwa ta Arbat Dam ta ɓalle kana ta yi ambaliya a dukkan ƙauyukan da ke yankin.

Ɗaruruwan mutane sun tsere zuwa yankunan da ke saman tsauni domin ambaliyar ruwan ko da yake ambaliyar ruwan ta rutsa da mutane da dama, a cewar wata jaridar da ake wallafawa a Sudan mai suna Al-Taghyeer.

An gina madatsar ruwan a 2003 saboda adana ruwa don amfani da shi a lokutan rani, sai dai an kwashe shekaru da dama ba a gyara ta ba.

AA