Abdourahamane Tchiani ya ce yana sa ran hadakar da Nijar ta yi da Mali da Burkina Faso za ta taimaki yankin na Sahel.

Shugaban mulkin soja na Nijar Janar Abdourahamane Tchiani ya bayyana cewa suna sane da cewa Faransa ce ke tunzura ECOWAS take saka musu takunkumi.

Janar Tchiani ya fadi hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na kasar cikin harshen Hausa, inda ya kara da cewa babu wani amfani da kasashen Nijeriya ko Senegal ko Benin ko Ivory Coast za su samu idan aka saka wa Nijar takunkumi.

Shugaba Tchiani ya jaddada cewa suna sane da cewa ta’addanci kawo musu shi aka yi, kuma wadanda suka kawo shi ko da sun bar kasar ba za su bar nufinsu ba.

"Sharrin da suka shuka mana, suka ci amanar kasashenmu, Allah ba zai bar su ba, Allah zai saka mana," in ji shi.

Labari mai alaka: Bayanai kan shugaban juyin mulkin Nijar Abdourahamane Tchiani

“Faransa ce ke son cimma wata manufa, ta ga zuwanmu zai katse mata tabbatar da wannan manufa,” in ji Tchiani.

Ya kuma jaddada cewa sojojin Faransa da ke Nijar suna daf da barin kasar, lokaci kawai suke jira.

“Sojawa na bisa hanyar tafiya, da yardar Allah za su bar kasar Nijar, lokaci ne idan ya yi za su tafi.

Dangane da makomar dangantakar da ke tsakanin gwamnatin Nijar da Faransa kuwa, Shugaba Tchiani ya bayyana cewa game da mu’amala ta al’ada, duk yadda Faransa ta ga dama haka za a yi, amma batun tattalin arziki, Nijar ke da iko da arzikinta.

“Arzikin kasar Nijar na ‘yan Nijar ne, muna da ‘yanci kansa kuma ‘yanci ba a baki ba na tabbas ne,” in ji Janar Tchiani.

Ya bayyana cewa za su dauki duka wasu matakan da za su iya dauka domin ganin ‘yan kasar Nijar sun amfana da arzikin da suke da shi.

Ya kuma bayyana cewa ‘yan kasar Nijar ne kadai za su iya yanke hukunci da kuma bayar da tabbaci kan ko nan gaba Nijar za ta iya hulda da Faransa.

“Hulda tsakaninmu da kasar Faransa dole sai mun koma wajen ‘yan kasa mu ji mene ne ra’ayinsu, lokacin murdiya ya ƙare, komai sai ‘yan kasa sun amince za a yi,” in ji shi.

Janar Tchiani ya mayar da martani kan yarjejeniyar da Nijar ta kulla da Burkina Faso da Mali ta Liptako Gourma, inda ya ce za su hada kansu domin su taimaki juna musamman ta bangaren tsaro.

A cewarsa, hadin kan na talakawa ne kuma idan talakawa suka hada kai za a samu tsaro inda ya ce "sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi."

Janar Tchiani ya gode wa kasashen Mali da Burkina Faso sakamakon bude musu iyakoki bayan da Nijeriya ta rufe, inda ya ce idan da ba su yi musu haka ba da yanzu ba su san inda suke ba.

TRT Afrika da abokan hulda