An kafa ƙungiyar platform ne a 2019 bayan an yi nazari a kan kundayen digirin da aka rubuta a harshen Turkanci don fayyace maudu'an da suka kamata a tattauna a kansu./Hoto: AA

Ɗalibai ƴan Afirka da ke karatu a Turkiyya sun gudanar da taro mai taken 1st Prafrica Workshop, ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar Platform, a Istanbul, don tattaunawa kan ƙalubalen da ke fuskantar nahiyar -- daga batun kiwon lafiya zuwa ƙirƙirarriyar basira da tattalin arziki da kuma siyasa.

Souandaou Athoumani Ali, wani ɗalibi ɗan ƙasar Comoros da ke karatu a Istanbul University kuma shugaban ƙungiyar ta Platform ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa sun gudanar da taron ne domin yin musayar ra'ayoyi kan yadda za su shawo kan tarin ƙalubalen da ke fuskantar nahiyarsu.

An kafa ƙungiyar platform ne a 2019 bayan an yi nazari a kan kundayen digirin da aka rubuta a harshen Turkanci don fayyace maudu'an da suka kamata a tattauna a kansu, in ji Ali.

Ya ƙara da cewa babbar manufar taron ita ce gabatar da sabbin bayanai game da ilimin da ƴan Afirka suke samu a Turkiyya wanda za su yi aiki da shi don gudanar da bincike a fannin kimiyya da sauran ɓangarori.

Mahalarta taron sun gabatar da maƙaloli a kan fannonin da suka haɗa da siyasa da kiwon lafiya da ƙirƙirarriyar basira da tattalin arziki inda suka mayar da hankali kan samar da hanyoyin shawo kan matsaloli rin su cututtuka masu yaɗuwa da rashin daidaito a siyasa.

Abdoul Fathi Sanogo, ɗan ƙasar Burkina Faso wanda shi ne babban mai tsare-tsare na the Platform, ya ce sun kafa ƙungiyar a watan Mayun da ya gabata kuma ta ƙunshi masu bincike ƴan Afirka.

AA