Akalla ɗalibai 22 ne suka mutu a ranar Juma’a bayan da ginin wata makaranta da ke tsakiyar birnin Jos ya rufta a kan ɗaliban da ke rubuta jarrabawa, a cewar gwamnatin jihar Filato da ke tsakiyar Nijeriya.
Kazalika mutum 132 ne suka jikkata sakamakon wannan iftila'i, in ji wata sanarwa da Kwamishinan Watsa Labarai na jihar Musa Ashoms ya fitar ranar Juma'a da maraice.
Ya ce an garzaya da waɗanda suka jikkata wasu asibitocin birnin na Jos inda ake kula da lafiyarsu.
Tun da farko sakataren hukumar bayar da agaji ta Red Cross reshen jihar Filato Nurudeen Hussaini Magaji ya shaida wa TRT Afrika cewa mutum 21 suka rasu sakamakon lamarin.
An jiyo ɗaliban da suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzai suna kukan neman agaji a makarantar ta Saint Academy da ke ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.
‘’Galibin waɗanda lamarin ya rutsa da su 'yan shekara 10 zuwa 13 ne," a cewar Magaji. Ya bayyana lamarin a matsayin mai ‘’tayar da hankali’’.
Masu aikin ceto sun yi ta ƙoƙarin zaƙulo waɗanda lamarin ya rutsa da su yayin da iyaye ke neman ‘ya’yansu.
Wani mazaunin wurin Chika Obioha ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa ya ga aƙalla gawarwaki takwas a wurin kuma wasu da dama sun jikkata.
"Kowa yana taimakawa don ganin ko za mu iya ceton mutane da yawa," in ji shi.
Ba a dai bayyana dalilin rugujewar ginin ba amma mazauna yankin sun ce ya biyo bayan ruwan sama kamar da bakin ƙwarya na kwanaki uku da aka yi a Filato ne.
Rushewar gine-gine ya zama ruwan dare gama gari a Nijeriya, ƙasar da ta fi yawan al'umma a Afirka, lamarin da ƙwararru suke dangana shi da rashin aiwatar da ka'idojin gini, da sakaci da kuma amfani da kayayyaki marasa inganci.
Aƙalla mutum 45 ne suka mutu a shekarar 2021 bayan da wani dogon bene da ake ginawa ya ruguje a gundumar Ikoyi da ke babban birnin tattalin arzikin Nijeriyar, Legas.
Sannan mutum 10 ne suka mutu sakamakon ruftawar wani gini mai hawa uku a unguwar Ebute-Metta da ke Legas shekara guda bayan haka.