Kuɗin-cizo wasu ƙananan ƙwari ne da suka fi maƙalewa a jikin katako ko shimfiɗar kwana. Hoto: OTHERS

Hukumomin Aljeriya sun sanar da cewa suna ɗaukar ƙwararan matakan lafiya a kan iyakokin ƙasar don hana kuɗin-cizo shiga ƙasar daga Faransa, ƙasar da a kwanan nan suka mamaye biranenta.

A wata sanarwa da Ma'aikatar Lafiya ta Aljeriya ta fitar ranar Alhamis ta sanar da "ɗaukar ƙwararan matakan lafiya don hana yaɗuwar duk wata annoba."

Ma'aikatar, ƙarƙashin haɗin gwiwa da hukumomi da dama sun ƙaddamar "da matakan sa ido da lura don hana shigar kuɗin-cizon."

A cewar ma'aikatar, matakan sun haɗa da "bin ƙwaƙƙwafin hanyoyin lafiya da feshin maganin ƙwari a jiragen sama da na ruwa da motocin sufuri musamman a lokutan da ma'aikatan cibiyoyin kan iyaka suka lura da wata barazana. "

Ministan Lafiya na Aljeriya Abdelhak Saihi ya ƙaryata labarin da aka yaɗa ranar Talata cewa kuɗin-cizo sun shiga ƙasar ta Arewacin Afirka.

Tashin hankalin da ya samu Faransa

Kuɗin-cizo sun yaɗu a biranen ƙasar Faransa, lamarin da ya jawo fargaba a tsakanin ƴan Aljeriya kan yiwuwar ƙwarin za su iya shiga ƙasarsu, ganin yawan mutanen da ke kai kawo a tsakanin ƙasashen biyu.

A ranar Talata ne Ministan Lafiya na Faransa Aurelien Rousseau ya nemi al'umma da ka da su ta da hankulansu a kan yaduwar kuɗin cizon.

A farkon makon nan ne gwamnatin Faransa ta sha alwashin ɗaukar matakai tare da "tabbatar da cewa za ta kare" al'ummarta daga annobar kuɗin-cizon.

Gomman bidiyoyin da aka wallafa a shafukan sada zumunta da dama sun nuna yadda kuɗin-cizon ke yaɗuwa a motocin bas-bas da jiragen ƙasa da filayen jiragen sama da sauran wuraren taruwar al'umma a Paris.

Gasar Wasannin Olympic

Annobar yaɗuwar kuɗin-cizon na zuwa ne a lokacin da Faransa ke shirye-shiryen karɓar baƙuncin Gasar Wasannin Olympic ta 2024 a Paris.

Kuɗin-cizo wasu ƙananan ƙwari ne da suka fi maƙalewa a jikin katako ko shimfiɗar kwana, kuma sukan hau jikin mutane ko dabbobi su sha jini, sannan cizonsu yana da ƙaiƙayi sosai, kuma suna saurin hayayyafa a cikin gidaje ko wuraren da mutane ke zama.

AA