A ganawar da suka yi a ranar Laraba, sun tattauna kan dangantakar kasashensu, da kuma batutuwan shiyyoyi da na duniya baki daya.

"Alakar Turkiyya da Sudan na ci gaba da bunkasa a kowace rana kuma hadin kai tsakanin kasashen biyu zai kara karfi," in ji Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a yayin ganawarsa da shugaban majalisar mulkin kasar Sudan Abdel Fattah al Burhan a Gidan Turkiyya da ke birnin New York na Amurka.

A ganawar da suka yi a ranar Laraba, sun tattauna kan dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, da kuma batutuwan da suka shafi shiyyoyi da na duniya baki daya.

Har ila yau, a ranar Talata, yayin jawabinsa a babban taron MDD na shekara-shekara, Erdogan ya ce "Dole ne a kawo karshen rikicin da ake fama da shi a Sudan da wuri-wuri, kuma mu ƙara zage damtse wajen cim ma wannan buri."

Mummunan yanayi a Sudan

Kasar Sudan dai ta sha fama da fada tsakanin sojojin Sudan da kuma dakarun Rapid Support Forces (RSF).

Akalla mutum 12,260 ne aka kashe yayin da fiye da 33,000 suka jikkata a rikicin da ya fara a watan Afrilun 2023, a cewar alkaluman MDD.

Ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya OCHA ya ce a yayin da al'amura ke ci gaba da tabarbarewa a fadin kasar Sudan, ana tilasta wa mata da kananan yara da daukacin iyalai ƙaurace wa gidajensu, tare da barin komai.

OCHA ta ruwaito cewa a halin yanzu Sudan na fuskantar "mafi girman karancin abinci a cikin shekaru 20."

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya (IOM) ta ce tun bayan da aka fara yakin Sudan a watan Afrilun 2023, sama da mutum miliyan 7.7 ne suka rasa matsugunansu.

TRT World