Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano Mohammed Usaini ya tabbatar da cewa akwai kusan mutum 400 da ke tsare a gidan gyaran hali na Kurmawa da ke cikin tsananin wahala sakamakon rashin sanin tabbas na makomarsu.
Kwamishinan ya bayyana haka ne a wani taron ƙungiyar lauyoyi reshen Jihar Kano wanda aka gudanar a ranar Litinin.
Gumel ya bayyana cewa akasarin waɗanda ake tsare da su babu bayanansu na shari’a da kuma bayanai kan laifukan da suka aikata.
Haka kuma ya bayyana cewa akwai ƙarancin lauyoyi waɗanda za su taimaka da shari’ar ɗumbin mutanen da ake tsare da su.
CP Gumel ya ƙara da cewa akwai ƙarancin ababen more rayuwa waɗanda suka haɗa da wuraren kiwon lafiya da muhalli mai tsafta da ofisoshin ma’aikatan kula da gidan gyaran hali na Goron Dutse.
Kwamishinan ya ce akwai wani kwamiti na musamman da ‘yan sandan jihar suka kafa domin aiwatar da shirin nan na musamman na PDSS wanda ya ƙunshi neman ‘yanci da kuma tabbatar da adalci ga waɗanda ake tsare da su.
Ya ce kwamitin wanda ya ƙunshi ƙwararru daga ɓangaren shari’a sun kai ziyara gidajen gyaran hali na Janguza da Kurmawa sai kuma ofisoshin ‘yan sanda na Zango da Hotoro da Sharada.
Ya bayyana cewa an faɗaɗa ziyarar zuwa kotun majistare ta Nomansland da babbar kotun da ke kan titin Miller inda suka tattauna da masu ruwa da tsaki domin nemo mafita.