Akesan: Yadda aka gudanar da bikin ranar mata 'yan kasuwa a kudancin Nijeriya

Akesan: Yadda aka gudanar da bikin ranar mata 'yan kasuwa a kudancin Nijeriya

Mataimakin Shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya halarci bikin Akesan wanda aka gudanar a Jihar Ogun.
Ana gudanar da bikin Akesan a Jihar Ogun a duk shekara domin murnar mata 'yan kasuwa da shugabanni. / Hoto: TRT Afrika

Daga Ibraheem Abbas

Mataimakin Shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya halarci bikin ranar mata 'yan kasuwa karo na 37 da aka gudanar a kudancin kasar domin taya mata 'yan kasuwa da shugabanni murna.

An gudanar da bikin a garin Iperu da ke Jihar Ogun wadda ke kudu maso yammacin Nijeriya.

Wadanda suka halarci bikin sun saka kayayyakin gargajiya masu kyau domin bikin ranar ta Akesan. / Hoto: TRT Afrika

Akesan Baale Oja ita ce wadda ta kafa birnin na Iperu mai dumbin tarihi. Ta kasance jagora kuma 'yar kasuwa a karni na 14, kamar yadda tarihi ya nuna.

'Yan asalin Iperu maza da mata suna girmama wannan rana. Sun saka kayayyaki masu kyau inda suka taka rawa da gudanar da wakokin gargajiya da rayae-raye.

Hadin kai

Shettima ya ce wannan bikin na shekara-shekara na taimakawa wurin hadin kan jama'ar Iperu.

"Wannan bikin yana nuna irin karfin da muke da shi idan muka zabi hada kanmu karkashin tarihinmu," kamar yadda mataimakin shugaban kasar ya bayyana.

An gudanar da wakoki da raye-raye a bikin Akesan na 2023 wanda aka gudanar a Jihar Ogun. / Hoto: TRT Afrika

Gwamnan Jihar Ogun Prince Dapo Abiodun ya bayyana cewa jama'ar Iperu na ci gaba da farfado da halaye nagari na Akesan.

Sauran muhimman mutanen da suka halarci wannan bikin sun hada da Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas da AbdulRasaq na Kwara da Yahaya Bello na Kogi.

Haka kuma Kakakin Majalisar Wakilan Nijeriya Tajudeen Abbas shi ma ya halarci wannan bikin.

Ranar Akesan na taimakawa wurin hada kan jama'ar Iperu, / Hoto: TRT Afrika
TRT Afrika