Hukumar tsara jarrabawar kammala makarantar sakandare ta WAEC a Ghana ta riƙe sakamakon wasu ɗalibai daga makarantu 235 kan zarginsu da satar amsa ta hanyar amfani da ƙirƙirarriyar basira AI.
Hukumar ce ke gudanar da jarabawar karshe a manyan makarantu a kasashe biyar masu amfani da Turancin Ingilishi wato Nijeriya da Ghana da Saliyo da Laberiya da Gambia - waɗanda ke tantance cancantar shiga manyan makarantu a ƙasashen.
A ranar Litinin ne aka sanar da sakamakon ɗalibai 448,674 waɗanda suka zana jarabaawar ta WAEC daga tsakanin watan Yuli zuwa na Satumba.
Ana zargin waɗanda aka riƙe musu sakamakon da amfani da ƙirƙirarriyar basira wajen gano amsoshin tambayoyin jarabawar.
Shugaban sashen hulɗa da jama'a na hukumar, John Kapi ya ce "Har yanzu ana bincike kan waɗannan matsaloli."
An soke sakamakon jaranawar wasu ɗalibai 3,647 ne saboda haramta musu shiga ɗakin jarabawa da kayayyaki, yayin da wasu 839 kuma aka soke jarabawarsu saboda samun su da wayoyin hannu a lokacin da suke rubuta jarabawar.
"Ɗalibai 448,674 da suka haɗa da maza 212,453 da mata 236,221 daga makarantu 975 ne suka zana jarrabawar. Wannan adadi ya zarce kashi 5.8% sama da na shekarar 2022 mai yawan 422,883," in ji Mista Kapi a cikin wata sanarwa.
An yi ta kiraye-kirayen hana amfani da ƙirƙirarriyar basira a fadin duniya, inda ƙwararru a harkar ilimi suka damu game da yiwuwar tasirin da kuskuren yin amfani da sabbin abubuwa za su yi a kan ilimi da binciken ilimi.