Gwamnatin Afirka ta Kudu ta yi wa jakadanta na Isra'ila da jami'an diflomasiyyarta na kasar kiranye, tana mai Allah-wadai da ruwan bama-bamai da Isra'ila take kan yankin Gaza na Falasdinu, abin da ta kira da "kisan kare-dangi."
Haka nan gwamnatin ta yi barazanar daukar mataki kan jakadan Isra'ila a kasar, bisa kalamansa kan matsayar Afirka ta Kudu game da yakin Isra'ila da Falasdinu.
Sai dai ba a samu karin bayani game da kalaman ba.
Yakin ya barke ne bayan da kungiyar 'yan tirjiya ta Falasdinu, wato Hamas ta kai hari kan Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya janyo mutuwar mutum 1,400.
Hare-haren Isra'ila kan Gaza ya hallaka sama Falasdinawa sama da 10,000, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta yankin Gaza ta aka yi wa ƙawanya.
"Gwamnatin Afirka ta Kudu ta yanke hukuncin janye jakadanta na Isra'ila da jami'an diflomasiyyarta da ke Tel Aviv babban birnin Isra'ila, domin yin tattaunawa," kamar yadda wani minista da ke fadar shugaban kasa, Khumbudzo Ntshavheni.
Ta kara da cewa majalisar zartarwar kasar ta lura da "kausasan kalaman jakadan Isra'ila a Afirka ta Kudu game da wadanda suke adawa da ta'addanci da kisan kare-dangin da gwamnatin Isra'ila take aikatawa", kuma cewa an umarci sashen huldar kasa-da-kasa ya "dauki matakan da suka dace ta hanyoyin diflomasiyya kan abin (da ya yi)."
Ntshavheni ta kara da cewa abin da jakadan Isra'ila a kasar ba abin 'lamunta' ba ne."
Zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa
Masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa, wadanda suke taruwa a gaban ofishin jakadancin Amurka da ke Johannesburg, da na Isra'ila da ke Pretoria da Cape Town. Sun yi kira ga gwamnatin Afirka ta Kudu da ta kori jakadan Isra'ila.
Ministan harkokin waje na Isra'ila Naledi Pandor, wanda a ranar Litinin ya karbi bakuncin jakandan Ukraine, Dmytro Kuleba, ya ce za a janye jami'an Afirka ta Kudu daga Tel Aviv, don su bai wa gwamnati cikakken bayani game da halin da ake ciki a yankin.
Pandor ya ce, "Muna bukatar samun daidaito da jami'anmu saboda muna da matukar damuwa game da cigaba da kisan yara da fararen hula a yankuna Falasdinu, kuma mun yi imanin cewa matakin Isra'ila ya zama hukuncin kan mai uwa da wabi".
Gwamnatin Afirka ta Kudu, wadda jam'iyyar ANC take jagoranta wadda kuma take da kusanci da Falasdinu, ta yi kira da a gaggauta tsagaita wuta a Gaza, kuma a bari a shiga da kayayyakin agaji zuwa yanki da ya sha ruwan bama-bamai.
Afirka ta Kudu ta shiga sahun kasashen da suka yi wajakadunsu kiranye daga Isra'ila don nuna adawa da hare-haren Gaza. Kasashen sun hada da Chile da Colombia da Honduras da Chadi.
Bolivia ta yanke huldar jakadanci da kasar. Israel ta soki kasashen Latin Amurka a makon baya, kuma ta yi kira ga Colombia da Chile da su "gagauta bayyana yin alla-wadansu kan Hamas".