Afirka ta Kudu na neman "ci gaba da kulla alaka bayyananniya" da Amurka kan batutuwan yankuna "bisa doron girmama juna", in ji Ministan Harkokin Waje Ronald Lamola.
Lamola ya bayyana haka a ranar Alhamis bayan kammala ziyarar da ya kai Amurka.
Ya isa Washington a makon da ya gabata a yayin da ake yada jita-jitar cewa jami'an diflomasiyyar Isra'ila na rokon 'yan majalisar dokokin Amurka su tirsasa wa Afirka ta Kudu ta janye karar kisan kiyashi da ta kai Tel Aviv a Kotun Kasa da Kasa (ICJ).
Afirka ta Kudu ta kai Isra'ila kara Kotun kasa da Kasa saboda hare-haren kan mai uwa da wabi da take kaiwa Gaza da aka mamaye wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 41,200 tun watan Oktoban bara.
Lamola ya gana da manyan masu ruwa da tsaki a Washington, ciki har da kwamitin Majalisar Wakilai Kan Afirka, Kwamitin Bakaken Fata, Kungiyar 'Yan Kasuwar Amurka da kungiyoyi masu zaman kansu.
'Yarda da sabanin ra'ayi'
Ministan harkokin wajen ya jaddada muhimmancin cigaban sauyin da ake samu a alakar da ke tsakanin Afirka ta Kudu da Amurka, inda ya kuma zayyano fannonin da ake hada kai.
"Ana matsa wa gaba, za kuma a bi hanyoyin dorewar tasarin dangantakar siyasa a koyaushe," in ji Lamola.
Da yake jawabi ga Babban Taron Shekara-Shekara Karo na 53 na 'Yan Majalisar Dokoki Bakaken Fata a Washington a makon da ya gabata, Lamola ya bayyana cewa "Mu yi mu'amala duk da bambance-bambance amma kuma dole mu yarda ana iya saba wa juna."
Ya ce "Ba za mu fada wa Amurka abinda za ta yi ko me muke tsammani ta fada mana mu yi ba."