Adadin waɗanda suka mutu a zaftarewar ƙasa a Ethiopia ya kai 229 yayin da ma'aikatan ceto suke ci gaba da zaƙulo mutane daga cikin ƙasa.
Sun riƙa amfani da shebura da hannayensu wajen zaƙulo waɗanda suke da sauran numfashi ranar Talata bayan zaftarwar ƙasar da ta faru a wani yanki mai nisa a kudancin Ethiopia.
Wannan shi ne bala’i mafi muni da aka fuskanta a ƙasar ta Kusurwar Afirka a baya bayan nan.
Mutane sun taru a wajen da bala’in ya faru, wanda yanki ne a ƙurya kuma mai tsaunuka a jihar Kudancin Ethiopia, yayin da wasu mutanen suke tono a cikin jar ƙasa, kamar yadda hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta suka nuna.
Lamarin ya faru ne a yankin Kencho-Shacha a Gundumar Gofa ranar Litinin kuma ya jikkata ɗaruruwan mutane, a cewar Sashen Yaɗa Labarai na yankin a cikin wata sanarwa.
An fito da mutum biyar da ransu daga cikin ɓaraguzai kuma suna samun kulawa a wata cibiyar kula da lafiya, a cewar kafar watsa labaran Gwamnatin Ethiopia.
Masu ceto na daga waɗanda abin ya rutsa da su
"A farko dai gidaje huɗu ne abin ya rutsa da su, daga baya an nemi agajin mutanen gidaje a yankin don ceton rayuka," kamar yadda wani darakta a Hukumar Kula da Annoba ta Ethiopia Kencho-Shacha ya shaida wa AFP.
"Amma su ma sun ɓata lokacin da ƙasa tarufta da su," a cewarsa, yana mai ƙara wa da cewa ruwan saman da ake yi kamar da bakin ruwan ƙwarya a yankin tun ranar Lahadi shi ne ya haifar da bala'in.
Kafar yaɗa labaran ƙasar ta ambato wani jami'in yankin Dagemawi Ayele yana cewa daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su akwai jami'an yankin da malaman makaranta dama'aikatan lafiya da ma'aikatan noma da suka yi gaggawar kai agaji.
Hotunan da hukumomin Gofa suka wallafa a kafofin sada zumunta sun nuna mutanen yankin suna ɗauko gawawwaki a gadon ɗaukar marasa lafiya, wasu kuma an nannaɗe su da leda.
Ethiopia,ƙasa ta biyu mafi yawan al'umma a Afirka da ke da kimanin mutum miliyan 120, tana yawan fuskantar matsalolin sauyinyanayi, ciki har da ambaliyar ruwa da fari.
"Na matuƙar damu da mummunan rashin da aka yi," a cewar Firaministan Ethiopia Abiy Ahmed kamar yadda ya wallafa a shafin X.
"Sakamakon abin da ya faru, an tura jami'an ko-ta-kwana na kare afkuwar bala'o'i ta Tarayya zuwa yankin, kuma suna aiki don rage tasirin bala'in."
Shugaban Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat ya ce "muna yin addu'o'in ga waɗanda abin ya shafa da iyalansu."