Adadin mutanen da suka mutu a Nijeriya sakamakon zazzaɓin Lassa mai saurin kisa ya ƙaru zuwa mutum 163 a ranar Alhamis.
Cutar zazzaɓin Lassa na ci gaba da yaɗuwa a jihohi 34 har da babban birnin tarayya Nijeriya Abuja, a cewar wata sanarwa da Cibiyar Yaki da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta ƙasa (NCDC) ta fitar.
A baya dai gwamnatin Nijeriyar ta bayyana cewa an gano wasu magunguna guda uku da za a yi amfani da su domin magance cutar.
An fi samun yaɗuwar zazzaɓin a lokutan rani, inda yawanci yakan soma ne daga watan Nuwamba zuwa Mayu na ko wace shekara.
A shekarar 2023, an samu jimillar mutane 1,227 da suka kamu da zazzaɓin Lassa, sannan mutane 219 sun rasa rayukansu sakamakon cutar.
Ana samun ɓullar zazzaɓin Lassa a ƙasashen Afirka da dama kamar Mali da Togo da Ghana da Laberiya da kuma Saliyo.
A shekarar 1969 aka fara samun ɓullar cutar a Nijeriya a jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin ƙasar.
A ranar 23 ga watan Janairu na 2019, gwamnatin Nijeriya ta kafa dokar ta-ɓaci sakamakon ɓarkewar zazzaɓin Lassa a ƙasar.
Ana kamuwa da cutar ne ta hanyar najasar ɓera, sannan tana iya yaɗuwa daga mutum zuwa mutum, haka kuma tana iya haifar da zazzaɓi da ke saurin kisa.
Hukumomin ƙasar na daɗa gargaɗin al'umma da su guji cuɗanya da ko wane irin nau'in ɓera.