CODECO na ɗaya daga cikin ɗimbin tsagerun da ke yaƙi kan filaye da albarkatu a gabashin DRC. / Hoto: Reuters

An kashe fararen-hula 80 a wani hari da ƙungiyar CODECO da ke ɗauke da makamai take kai a cikin dare a wasu jerin ƙauyuka a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo a farkon makon nan, in ji tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya MONUSCO a ranar Alhamis.

Sabon adadin waɗanda suka mutu ya zarce ƙiyasin da aka yi a baya na akalla mutum 51, wanda hukumomin yankin suka bayyana kai tsaye bayan harin da aka kai cikin dare a ranar Litinin a yankin Djugu, na lardin Ituri.

MONUSCO ta ce ta tura dakarun wanzar da zaman lafiya domin dakile harin cikin gaggawa, sai dai ta ce amfani da makamai masu kaifi da mayakan ke yi a maimakon manyan bindigogi ya kawo tsaiko wajen mayar da martani.

Ko a lokacin da dakarun wanzar da zaman lafiya suka isa, “abin takaicin tuni suka kashe fiye da fararen hula 80 tare da ƙona idaje da cusa tsoro a zukatan jama’a, in ji ƙungiyar ta MDD.

CODECO na ɗaya daga cikin ɗimbin tsagerun da ke yaƙi kan filaye da albarkatu a gabashin DRC.

Tana kai hare-hare a kai a kai kan sansanonin ‘yan gudun hijira, wadanda ke tayar da ƙayar baya tun bayan ci gaba da faɗaɗa yaƙi da ‘yan tawayen M23 ke yi da Rwanda ke marawa baya.

Yunkurin M23 daga lardin Kivu ta Arewa zuwa lardin Kivu ta kudu na barazanar haifar da bala'in jin kai, in ji jami'an yankin.

Reuters