Gwamnonin jihohin Arewacin Nijeriya sun sha alwashin bunƙasa harkar ilimi da fasaha da kula da lafiya da kuma ayyukan walwalar jama'a domin magance matsalar rashin tsaro da yankin ke fama da ita.
Gwamnonin sun yi wannan alkawari ne a taron da suka yi a jihar Kaduna a ranar Talata, ƙarƙashin inuwar ƙungiyarsu ta Gwamnonin Arewa.
Ga dai wasu muhimman abubuwa da gwamnonin suka tattauna a taron, kamar yadda jawabin bayan taro da mai taimaka wa gwamnan jihar Gombe wanda shi ne shugaban ƙungiyar, kan watsa labarai ya fitar.
1. Kungiyar ta yaba wa gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, "wanda ya nuna jajircewarsa wajen samun nasara a yaƙin da ake yi da ta'addanci, fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran laifuka."
2. Kungiyar ta nuna matukar tausayawa da goyon baya da ba da hadin kai ga gwamnatoci da al’ummomin Jihohin Kaduna da Katsina da Neja da Filato da Zamfara kan kalubalen tsaro da ba a taba ganin irinsa ba a halin yanzu da ya addabe su, a wannan mawuyacin lokaci.
3. Taron ya yi nuni da cewa yana da matukar muhimmanci a mayar da hankali wajen haɓaka ayyukan ci gaban al’umma da yankin baki ɗaya, tare da nuna damuwa cewa a halin yanzu yankin yana fama da matsaloli kamar na yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a duniya.
A don haka ne, gwamnonin suka sha alwashin saka hannun jari mai tsoka a fannin ilimi da bunkasa fasaha da kula da lafiya da kuma ayyukan jin dadin jama'a domin magance matsalar.
4. Gwamnonin sun karbi rahoton wani kwamitin da zai duba rahoton hukumar New Nigeria Development Company (NNDC), sannan an yanke shawarar cewa mambobin kwamitin su yi nazarin rahoton a taron ƙungiyar gwamnonin na gaba.
5. Taron ya yi nuni da irin rawar da ake sa ran kamfanin New Nigeria Development Company (NNDC) zai taka wajen farfado da tattalin arzikin jihohin Arewa. A kan haka ne taron ya yanke shawarar saka hannun jari a cikin muhimman ababen more rayuwa wadanda za su iya bude manyan masana'antu da tattalin arzikin Arewa.
6. Taron ya yi nuni da cewa sauyin yanayi da rashin dorewar ayyukan noma da karuwar jama'a na haifar da gagarumin kalubale ga yankin.
Ya kuma ƙuduri aniyar daukar cikakken tsarin da zai inganta kiyaye muhalli da dauwamammen tsarin noma da kula da albarkatun kasa don kare rayuka da rayuwar jama'a da kuma kiyaye al'adun kasa har kan al’ummar da ba ta ma zo ba tukun.
7. Taron ya saurari bayanai daga shirin bunƙasa ilimin ƴaƴa mata da ƙarfafa musu (AGILE) da kuma wasu bayanan daga tawagar Bankin Duniya. Sannan ya bai wa shirin AGILE da tawagar Bankin Duniya tabbacin samun goyon bayan gwamnonin da kuma bukatar su da su hanzarta tsarin inganta shirin.
8. Taron ya kuma karɓi baƙuncin kwamitin zartarwa da kwamitin amintattu na Ƙungiyar Dattijan Arewa Consultative Forum (ACF). Kungiyar gwamnonin ta kuma yanke shawarar bayar da goyon baya da karfafa gwiwar kwamitin amintattun ACF wajen ganin an cimma manufofin shugabannin da suka kafa ta.
9. Gwamnonin sun kuma karɓi rahoto daga Gamayyar Kungiyoyin Arewa a kan tsaro a Arewacin Nijeriya. Kungiyar ta yaba wa gamayyar bisa jajircewarta wajen tabbatar da tsaron yankin Arewa tare da yin alkawarin hada kai da ita.
10. Kungiyar gwamnonin ta yaba wa shugabanninta kan hada hannu da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da shugabannin rundunar soji da gamayyar kungiyoyin farar hula na Arewa da sauran masu ruwa da tsaki wajen tsara hanyar samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Arewa.
11. Zauren ya yaba wa shugaban kungiyar bisa jajircewarsa wajen ciyar da muradun Arewa gaba. Kungiyar ta kuma yabawa mai masaukin baki Gwamnan bisa namijin kokarin da yake yi na karbar bakuncin tarukan dandalin.