Abubuwa shida da suka kamata ku sani game da sabuwar dokar ta-ɓaci kan ilimi ta Jihar Kano

Abubuwa shida da suka kamata ku sani game da sabuwar dokar ta-ɓaci kan ilimi ta Jihar Kano

An ware N300m don bai wa malaman firamare bashi mai sauƙin biya. Sannan an samar da manyan motocin bas 70 don kai yara mata makarantu.
Gwamna Abba ya ce  daga yanzu gwamnatinsa za ta duƙufa wajen gina dubban azuzuwa da ɗakunan bincike da bai wa malamai horo da saka yara kimanin 989,234 da ba sa karatu a makaranta./Hoto: Abba Kabir Yusuf/Facebook

Gwamnan Kano da ke arewacin Nijeriya ya ayyana dokar ta-ɓaci kan harkokin ilimi a wani mataki na farfaɗo da fannin ilimi a jihar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya jagoranci manyan jami'an gwamnati da masana harkokin ilimi da 'yan siyasa wajen ƙaddamar da dokar ta-ɓacin ranar Asabar a birnin Kano, ya ce babban burinsa shi ne samar da ilimi mai inganci ga kowa don ci gaban jihar.

''Samar da ilimi mai inganci shi ne babban makami na yaƙi da talauci da miyagun laifuka a cikin al'ummarmu," in ji Gwamna Abba.

A cewarsa, daga yanzu gwamnatinsa za ta duƙufa wajen gina dubban azuzuwa da ɗakunan bincike da bai wa malamai horo da saka yara kimanin 989,234 a makarantu.

''Wannan mataki zai taimaka wajen ceto makarantunmu da suka durƙushe, mataki ne mai tsauri sosai inda za a tabbatar da cewa kowane yaro a Jihar Kano ya samu ilimi mai inganci, wanda shi ne babban hakkinmu'', a cewar gwamnan.

Ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a fannin ilimin jihar su haɗa kai da gwamnati domin magance matsalolin da suke yi wa ɓangaren ilimin jihar tarnaƙi.

Ya ce: "Ina kira ga masu ruwa da tsaki da gwamnati da malamai da iyaye da kamfanoni masu zaman kansu da sauran al’umma su haɗa kai wajen farfaɗo da fannin ilimi domin ci gaban al’ummarmu."

Ga wasu muhimman matakai game da dokar ta-ɓaci a fannin ilimin Kano:

  • Garambawul ga dukkan makarantun firamare da ƙananan makarantun sakandare, tare da gina sabbin azuzuwa 1000 a ƙananan hukumomi 44 da ke jihar Kano

  • Kwaskwarima ga ɗakunan gwaje-gwajen kimiyya 300 tare da gina sabbin ɗakuna 300 a makarantu 200 da ke jihar. Jimilla, za a gina azuzuwa 28,264 a makarantun jihar daga yanzu zuwa shekaru uku.

  • Ɗaukar aiki na jami'ai 1000 a ɓangaren koyarwa da wanda ba na koyarwa ba a makarantun gaba da sakandare da ke faɗin jihar. Tare da ɗaukar sabbin malamai 10,000

  • Gwamnati za ta biya dukkan ƙudin makaranta na tuition fee tare da bayar da satifiket ga ɗaliban da aka bai wa tallafin karatu (scholarship) a jami'o'in jihar. Sannan za a biya kuɗin NECO da NBAIS ga ɗaliban da suka cancanta.

  • Za a sake buɗe dukkan makarantun kwana da gwamnatin da ta gabata ta rufe. Sannan za a ba da abinci sau ɗaya kullum ga ɗaliban firamare, da inifam kyauta.

  • An ware N300m don bai wa malaman firamare bashi mai sauƙin biya. Sannan an samar da manyan motocin bas 70 don kai yara mata makarantu.

TRT Afrika