Ranar farko ta zanga-zangar da aka fara a Nijeriya ta bar baya da ƙura, inda rahotanni daga sassan ƙasar suke nuna yadda aka samu asarar rayuka da dukiyoyi, da kuma ɓarnata kadarorin gwamnati da ma na al'umma.
A ranar Alhamis ne zanga-zangar ta kankama a faɗin ƙasar, bayan shafe makonni ana shirya mata, don kokawa kan tsadar rayuwa a ƙasar, inda aka yi mata taken "a kawo ƙarshen rashin iya mulki" a Nijeriya.
Dubban mutane a birane daban-daban na Nijeriya ne suka hau kan tituna domin bayyana ɓacin ransu kan matsin rayuwar da suke ciki wanda ya yi ƙamari tun hawan Shugaba Bola Tinubu kan mulki a shekarar 2023.
Suna riƙe da kwalaye da aka yi rubutu kamar "A kawo ƙarshen yunwa a Nijeriya", "A dawo da tallafin man fetur" da sauransu. A Abuja, babban birnin Nijeriya, masu zanga-zangar sun hau manyan tituna duk da umarnin da wata kotu ta bayar na taƙaita zanga-zangar a Babban Filin Wasa na Ƙasa.
Ga abubuwan da suka fi ɗaukar hankali game da zanga-zangar da ta gudana a jihohi da dama na ƙasar.
Asarar rayuka
Bayanai sun nuna cewa an samu asarar rayuka a jihohi da dama da suka haɗa da Borno da Kano da Kaduna da Nasarawa. Ko da yake kawo yanzu hukumomi ba su fitar da cikakkun alƙaluman ba, amma ganau sun shaida mana cewa an rasa rayuka sama da bakwai a jihar Kano kaɗai. Haka kuma gwamnatin Jihar Borno ta ce an kashe mutum huɗu. Kazalika Babban Sifeton 'yan sandan ƙasar Kayode Egbetokun ya bayyana cewa an kashe ɗan sanda ɗaya tare da jikkata da dama a yamutsin.
Sata da ɓarnata dukiya
Wasu rahotanni a jihohin kamar Kano da Kaduna, an ruwaito yadda dandazon masu iƙirarin zanga-zangar suka shiga fashe-fashen shaguna don satar kayayyaki da dukiyoyin jama'a.
A Kano, wasu masu zanga-zangar sun kai hari kan wurare daban-daban, ciki har da cibiyar horarwa kan fasahar zamani ta gwamnatin tarayya wadda ake shirin ƙaddamarwa nan ba da jimawa ba.
Bidiyoyi da aka watsa a shafukan intanet sun nuna yadda masu zanga-zangar riƙa wasoson kayan da ke cikin cibiyar.
Sannan masu zanga-zangar sun fasa shaguna da kantuna inda suka riƙa satar kayayyaki.
Rundunar 'yan sandan jihar ta Kano ta ce ta kama mutum 269 da hannu kan satar kayayyakin jama'a a yayin zanga-zangar.
A jihar Kaduna ma, an ga hotunan wasu masu zanga-zangar na yin ta'adi a ofishin hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar. An farfasa tagogin gilashi na ginin, kuma an ce an wawashe wasu kayyakin hukumar.
Dokar hana fita
An samu arangama tsakanin 'yan sanda da ɗaruruwan masu zanga-zanga a birnin Kano da ke arewacin Nijeriya da ma wasu jihohin ƙasar, inda aka riƙa harba tiyagas bayan da wasu mutane suka riƙa rikiɗe zuwa fashe-fashe da satar kayayyaki.
Gwamnatin jihar Kano ta sanar da kafa dokar hana zirga-zirga ta nan-take a faɗin jihar tsawon awa 24, sakamakon rikiɗewar zanga-zangar.
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ce wannan mataki ya zama wajibi domin shawo kan tarzomar da ta ɓarke inda wasu ɓata-gari suka riƙa fashe-fashe da wasoson kayayyaki.
Kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya faɗa cewa an ɗauki matakin ne bayan taron gaggawa na majalisar tsaro ta jihar, don guje wa ta'azzarar lamarin. Gwamnati ta yi kira da al'umma su haɗa kai don hana azzalumai yin ta'asa a jihar.
A jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya, gwamnati ta sanya dokar hana fita ta awa 24 a faɗin domin hana zanga-zangar rikiɗewa zuwa tarzoma.
Wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan jihar ASP Nahum Kenneth ya fitar ranar Alhamis ta ce sun ɗauki matakin ne domin tabbatar da doka da oda sakamakon zanga-zangar da ke faruwa a faɗin Nijeriya kan tsadar rayuwa.
Kazalika gwamnatin jihar Nasarawa ta sanya dokar hana fita a ƙaramar hukumar Karu mai maƙwabtaka da Abuja sakamakon ɓarkewar tazoma.
Haɗin-kan jama'a
Yayin da a Legas, babban birnin kasuwanci na Nijeriya aka ruwaito cewa mutane sun fito sun yi tattaki cikin luman, a birnin Jos na jihar Filato, an ga hotunan jama'a mabiya mabambanta addinai sun haɗa kansu ba tare da tashin hankali ba.
A Lagos ɗin, masu zanga-zangar sun fantsama kan tituna a yankin Ikeja inda suka nufi gidan gwamnati domin bayyana rashin jin daɗinsu kan matsin rayuwar da ake ciki.
Wani hadimin gwamnan Legas kan kafafaen sada zumunta, Jubril Gawat ya wallafa wani bidiyon da shafina na X, inda ya ce masu zanga-zange sun yi amfani da dandalin Gani Fawehinmi Park da ke Ojota, kuma sun kammala cikin lumana.
An danganta nasarar zanga-zangar a waɗannan wurare kan kyakkyawan jagorancin matasan da suka aiwatar da tattakin.
Ƙaurace wa zanga-zanga
Rahotannin daga jihar Bayelsa da ke yankin Naija-Delta a kudancin Nijeriya, sun ambato gwmnan jihar Douye Diri yana yaba wa matasa a jihar kan ƙin shiga zanga-zangar da aka fara a yau.
Gwamnan ya ce rashin fitar matasan alama ce ta cewa suna da hikima da rungumar zaman lafiya. An ambato shi yana jawabi yayin tattakin da yake yi mako-mako mai suna "properity walk" don kyautata mu'amala da al'umma.
Haka a jihar Taraba da ke arewa maso gabas, rahotannin sun nuna yadda zanga-zangar ba ta samu karɓuwa ba, inda aka ga hotunan al'ummar Musulmai suna gabatar da sallolin neman daidaituwar lamura ga jama'a.